Gwamnatin Bauchi ta ce ba za ta lamunci kalaman da ka iya tunzura jama’a daga wajen duk wani malami mai wa’azi a jihar ba.
Sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Kashim ne ya yi wannan gargadin yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron kwamitin tsaron jihar, a ranar Litinin a Bauchi.
- Buhari zai tafi Saudiyya don yin Umararsa ta karshe a matsayin Shugaban Kasa
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da ’Yan Najeriya Ke Gudun Kayayyakin Da Aka Yi A Kasar
Wannan gargadi na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan kalaman Sheikh Idris Tanshi game da neman taimkakon Manzon Allah (SAW).
Kashim, wanda shi ne shugaban kwamitin tsaron, ya ce gwamnatin jihar za ta tunkari duk wani mai wa’azi da ya yi kalaman da za su iya kawo rarrabuwar kawunan jama’a.
Ya ce, “Muna farfadowa ne daga wani mawuyacin halin da aka tsinci kai na yakin neman zabe kuma bayan zaben akwai bukatar kara tsauraran matakan tsaro.
“Mun damu saboda wannan ba batun akida ba ne, ko siyasa, batun tunzura jama’a ne da ke iya haifar da rarrabuwar kawuna.
“Mun tattauna kuma mun yanke shawarar cewa Bauchi wuri ne mai matukar zaman lafiya kuma za mu yi duk abin da za mu iya don tabbatar da wannan zaman lafiyar.
“Ba za mu bari wani abu ko kalaman wani su kawo cikas ga zaman lafiyar da muke da ita a jihar ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma kuma, “Daga yanzu ba za mu kyale wani ya ci mutuncin wani ko cin mutuncin imanin wani ko wasu mutane dangane da imaninsu ba.”
Shi ma da yake jawabi, kwamishinan ’yan sandan jihar, Aminu Alhassan, ya bayyana cewa ana kokarin dakile abubuwan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.