✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wa’adin ECOWAS: Sojojin Nijar sun yi shirin ko-ta-kwana

Sojojin Nijar na fargabar kai musu hari daga dakarun ECOWAS.

Gwamnatin mulkik soji a Jamhuriyar Nijar ta rufe sararin samaniyarta bisa fargabar yiwuwar kai mata farmaki.

Wannan na zuwa ne bayan cikar wa’adin kwanaki bakwai da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta ba su a ranar Lahadi.

Mambobin ECOWAS sun samu rabuwar kai kan daukar matakin sojin, wanda shugaban kungiyar kuma na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukata.

Sai dai a wani yunkuri na kare kai daga shirin ECOWAS, shugaban dakarun sojin da ya jagoranci hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, Janar Abdourahamane Tchiani, ya nemi hadin kan kasar Rasha.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin Katsina, Kebbi da Jigawa a Fadar Gwamnatin Najeriya a wani yunkuri na daukar mataki a kan Nijar.

Tuni dai shugabannin kasashen duniya da dama suka yi Allah-wadai da juyin mulki da sojojin fadar shugaban kasar Nijar suka.

Kazalika, juyin mulki ya sanya kasashe da dama ciki har da Amurka da Faransa janye tallafi da suke bai wa Nijar.