✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwar ’ya’ya takwas ta samu digiri na uku

Wata uwar ’ya’ya takwas mai kimanin shekara 45 mai suna Halima Usman ta nuna cewa yawan iyali da kuma zaman aure ba sa hana neman…

Wata uwar ’ya’ya takwas mai kimanin shekara 45 mai suna Halima Usman ta nuna cewa yawan iyali da kuma zaman aure ba sa hana neman ilimi, inda ta samu digirinta na uku daga Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Saklkwato a makon jiya.

Halima Usman wadda ’yar asalin Jihar Kebbi ce takaranta digirinta na uku ne a fannin lissafi kamar yadda Gwamnatin Jihar Kebbi ta wallafa hakan a shafinta na tweeter domin taya ta murna.

Gwamnatin Kebbi ta rubuta a shafinta na tweeter@KBStGobt, cewa: “Wata mata mai ’yar shekara 45 wacce ta haifi ’ya’ya takwas daga Jihar Kebbi (mai suna) Halima Usman ta kammala digiri na uku a fannin lissafi. Kamar yadda bayanin ya zo a shafin a ranar 12 ga Afrilun bana.

Halima tana cikin daliban Jami’ar Usman Dan Fodiyo da aka yaye kwanakin baya inda aka ba ta takardar shaidar digiri na uku.