✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Uwa ta zargi ’yan sanda da sakin wanda ya yi wa ’yarta ’yar wata 20 fyade

Sai dai ’yan sanda sun musanta labarin, inda suka ce ba su da hurumi

Wata uwa a yankin Rugan Rafin Sidi a Hanwa da ke Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna, ta zargi ’yan sanda da sakin wanda ake zargin ya yi wa ’yarta ’yar wata 20 a duniya fyade.

Wadda ake zargin mai suna David Solomon, da shi da yarinyar duk suna zaune ne a unguwar ta Hanwa da ke Sabon Garin Zariya.

Sai dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta musanta cewa tana da hannu a sakin wadanda aka kama a kan zargin.

Kakakin rundunar a Jihar, DSP Muhammad Jalige, ya musanta zargin a lokacin da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho.

Ya ce ana yawan zargin ’yan sanda da da sakin wadanda ake tuhuma bayan sun gabatar da su a gaban kotu.

Jalige ya ci gaba da cewa dukkan mai laifin da ’yan sanda suka gabatar a gaban kotu sauran aikin ya koma hannun kotu, ya bar wajensu.

A cewarsa, ’yan sanda ba su kai mai laifi ko wanda ake tuhuma gidan yari saboda kotu ce kadai doka ya bata wannan iko.

%d bloggers like this: