Wata uwa a yankin Rugan Rafin Sidi a Hanwa da ke Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna, ta zargi ’yan sanda da sakin wanda ake zargin ya yi wa ’yarta ’yar wata 20 a duniya fyade.
Wadda ake zargin mai suna David Solomon, da shi da yarinyar duk suna zaune ne a unguwar ta Hanwa da ke Sabon Garin Zariya.
- Me ya sa ’yan Najeriya ke debe tsammani kan Super Eagles?
- INEC ta sanya ranar bai wa zababbun gwamnoni shaidar lashe zabe
Sai dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta musanta cewa tana da hannu a sakin wadanda aka kama a kan zargin.
Kakakin rundunar a Jihar, DSP Muhammad Jalige, ya musanta zargin a lokacin da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho.
Ya ce ana yawan zargin ’yan sanda da da sakin wadanda ake tuhuma bayan sun gabatar da su a gaban kotu.
Jalige ya ci gaba da cewa dukkan mai laifin da ’yan sanda suka gabatar a gaban kotu sauran aikin ya koma hannun kotu, ya bar wajensu.
A cewarsa, ’yan sanda ba su kai mai laifi ko wanda ake tuhuma gidan yari saboda kotu ce kadai doka ya bata wannan iko.