Bayan gabatar da wata kara a kotun Berks County Court da ke Jihar Pennsylvania a kasar Amurka, Babban Alkalin Kotun, Dennis Charles ya tuhumi wata mata mai suna Lisa Snyder mai shekara 37 kuma uwar ’ya’ya biyu da laifin rataye ’ya’yan kafin ta fara shirin yin lalata da karen gidansu.
Ana tuhumar Lisa da laifuffukan kisan kai da ci zarafin yara, inda aka gabatar da ita a kotu kan jawo mutuwar wata yarinya mai suna Brinley mai shekara hudu da wani mai suna Conner mai shekara takwas a gidansu da ke birnin Albany.
- Ya rayu shekara 53 da kudin karfe a cikin hancinsa
- ‘Yadda ’yan bindiga suke tilasta mana kwana a jamhuriyar Nijar kullum da yamma’
Mai shigar da karar ya ce, idan aka tabbatar da laifin Lisa game da kisan kai na farko za a yanke mata hukuncin kisa.
Mataimakiyar Shugaban Gundumar, Margaret McCallum ta ce Lisa ce kadai a gidan lokacin da aka gano yaran a rataye kuma ita kadai ce babba a cikin gidan inda aka yi amfani da wata roba aka rufe igiyar da ake daure karen.
Yaran sun rasu ne bayan samun raunuka kwana uku da rataye su sai dai a cewar Lisa yaran ne suka kashe kansu.
Sannan ta yi zargin cewa Conner ne ya kashe ’yar uwarsa sakamakon wulakanta shi da take yi a makarantarsu.
Sai dai hukumomi sun ce Conner bai nuna wata alamar fushi ba tun lokacin da suke hanyarsu ta dawowa gida a cikin bas a ranar da abin ya faru.
A matsayinmu na ’yan sanda muna bibiyar shafin sada zumunta na Lisa inda ake sa ran za a iya bankado wasu bayanai a gurbin aika sakonni na Facebook Messenger, ciki har da hotuna wadanda ana iya samun bayanai cewa matar na yin lalata da karen gidansu inda aka kwatanta shi a matsayin rashin hankali.
Za a ci gaba da sauraran karar a ranar 12 ga watan Fabrairun badi.