✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa ta kashe ’ya’yanta biyu a Kano

Ana zargin matar ta hallaka ’ya’yanta nata ne saboda mijinta ya kara aure

Ana zargin wata mata da kashe ’ya’yanta biyu sannan ta tsere a unguwar Sagagi da ke cikin birnin Kano.

Matar mai shekara 22 ta yi amfani da adda ne ta kashe ’ya’yan nata da suka hada da Yusuf mai kimani shekara shida da kanwarsa Zahra’u mai shekara uku a ranar Juma’a.

Wasu mazauna yankin na zargin matar ta aikata danyen aikin ne saboda takaicin kara auren da mijinta ya yi watanni ukun da suka gabata.

Shaidu sun ce wadda ake zargin ta kira mijin nata a waya cewa an kai mata hari gida, amma da ya je sai ya iske gawar yaran biyu, ita kuma ba a san inda take ba.

Wasu kuma sun shaida wa wakilinmu cewa makwabta sun yi kokarin dauki a cikin gidan bayan sun ji hayaniya.

Da isarsu sai suka iske wadda ake zargin ta ji wa wata makwabciyarta rauni har ta ranta a na kare.

Tuni dai aka garzaya da matar da ta ji wa rauni zuwa asibiti.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ba ta kai ga cewa komai ba tukuna.