Kotun Majistare da ke Kafanchan a Jihar Kaduna ta tsare wata mata mai shekaru 30 a gidan yari bisa zargin kashe jaririyarta ’yar watanni takwas ta hanyar shayar da ita maganin ɓera.
Hukumar Tsaro ta NSCDC ce ta gurfanar da ita bisa zargin aikata kisan kai, wanda ya saɓa wa Sashe na 189 na Dokar Laifuffuka ta Jihar Kaduna.
Mai gabatar da ƙara, Marcus Audu, ya shaida wa kotu cewa wani mai suna Godfrey Sunday daga unguwar Fadia Bakut, Zonkwa ne ya kai rahoton lamarin ofishin NSCDC a ranar 11 ga Disamba.
A cewar Audu, a ranar 10 ga Disamba, wacce ake zargi ta shayar da ’yarta da maganin bera.
An garzaya da jaririyar zuwa Babban Asibitin Zonkwa inda ta rasu a washegari.
An fara kai rahoton lamarin ne ga Cibiyar yaqi da cin zarafin mata da ƙananan yara mai suna Salama Sexual Assault Referral Center da ke garin Kafanchan, kafin daga bisani aka mika wa NSCDC don ci gaba da bincike.
Mai gabatar da kara ya ce wacce ake zargi ta amsa laifin da ake tuhumar ta da shi yayin gudanar da binciken.
Alkalin kotun, Samson Kwasu, ya ki yarda ya karbi kukan wacce ake tuhuma saboda rashin hurumin sauraron shari’ar.
Ya umurci masu gabatar da kara da su miƙa wa Daraktan Gurfanarwa na jihar Kaduna da takardun shari’ar don neman shawara a kai.
An ɗage shari’ar zuwa ranar 17 ga Disamba domin ci gaba da sauraro.