Hukumar ‘yan sandan jihar Enugu, ta fara binciken zargin wata mata mai suna Ijeoma Nnaji da ta kashe jaririnta mai shekara daya da wata biyar a kauyen Amankanu unguwar Amuri da ke Karamar Hukumar Nkanu ta Yamma jihar Enugu.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar SP Ebere Amaraizu, ne ya sanar da hakan a yau Lahadi, wanda ya ce lamarin ya faru ne ranar 30 ga watan Mayu 2019.
Matar da ake tuhuma da ake zargi ta kashe jaririn ne mai suna Chiemerie Nnaji na tsare a hannun ‘yan sanda.
A yanzu haka jaririn da aka kashe yana babban asibitin Agbani a jihar.