Shugaban Kasar Gabon, Mista Brice Oligui Nguema ya miƙa ƙoƙon bararsa ga attajirin Afirka Alhaji Aliko Ɗangote kan ya je ƙasarsa, ya kafa masana’antun takin zamani da na siminti.
Shugaban na Gabon ya ce, akwai damarmaki ga Kamfanin Ɗangote na zuba jari a fannin takin zamani, musamman takin Yuriya da kamfa (phosphate).
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da Ɗangote ya ziyarci ƙasar, inda suka gana da Shugaban da ƙusoshin gwamnati.
A lokacin Ɗangote ya buƙaci ƙasar ta bayyana masa yadda zai iya taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikinta, inda a nan shi Shugaban na Gabon ya ce, lallai akwai damarmaki a vangaren sarrafa taki da siminti.
Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da Ɗangote da wasu hukumomi a Nijeriya suke takun-saqa, musamman game da matatar mansa da ke Legas.