✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa ta kama mijinta yana lalata da ’yarsu a Gombe

An gurfanar da wani magidanci mai suna Muhammad Nurudden da ke zaune a Unguwar Barunde da ke garin Gombe fadar Jihar Gombe a gaban Kotun…

An gurfanar da wani magidanci mai suna Muhammad Nurudden da ke zaune a Unguwar Barunde da ke garin Gombe fadar Jihar Gombe a gaban Kotun Manyan Laifuffuka da ke Gombe, bisa tuhumarsa da laifin aikata lalata da ’yarsa (an sakaya sunanta).

Mutumin da ake tuhuma, matarsa mai suna Maryam Bitrus ce ta kama shi da kanta a lokacin da yake lalata da ’yar tasa ’yar shekara goma.

Da Aminiya take zantawa da yarinyar a harabar kotun, ta ce babanta yana kwanciya da ita kuma yakan dake ta. “Idan ya zo sai ya ce in zo. Idan na zo sai ya ce in kwanta, sai ya hau kaina. Idan ya gama sai ya ce idan na fada wa mamata zai dake ni,” inji yarinyar.

Yarinyar ta ce, “Shekaranjiya (ranar Litinin) ce ya zo ya ce in kwanta sai ya hau kaina. Yana kwance a kaina sai mamata ta kama shi.”

Mahaifiyar yarinyar mai suna Maryam Bitrus, mai shekara 25 ta bayyana cewa idan ta fita unguwa ne mijin nata yake lalata da ’yarsa, kuma ya ja mata kunne, ya ce idan ta fada mini zai dake ta. Ta ce a lokacin da ta kama shi na farko yana lalata da ’yar tasa sai ya roke ta kan cewa ta rufa masa asiri ba zai kara ba.

“Bayan wasu kwanaki sai na sake kama shi a karo na biyu, da kaina na ce ba ya nemi in rufa masa asiri ba a karon farko, me ya sa ya sake? A nan ne na ce ba zan bar shi ba, shi ne na sanar da makwabta abin da yake faruwa. Su kuma suka sanar da kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta ‘Human Right Coalition’ suka kama shi suka kai shi kotu,” inji mahaifiyar yarinyar.

Maryam Bitrus ta kara da cewa bayan  sake kama mijin nata ne ta sanar da mahaifiyarsa cewa ba za ta zauna da shi ba, za ta tafi gidansu, shi ne aka yi ta ba ta hakuri.

Muhammad Nurudden, bai musanta zargin da ake yi masa ba, inda a gefe guda ya ce yana yin haka ne domin ya bai wa uwar yarinyar haushi. Hakan ya sa Mai shari’a Saleh Jibrin Abubakar, bai fara sauraron karar ba ya ba da umurni kai-tsaye a tura shi kurkuku zuwa ranar Talata 3 ga Afrilu don fara sauraron karar. Haka kuma za a kai yarinyar asibiti domin duba lafiyarta saboda tana kukan cewa mararta tana ciwo.