✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu

An bai wa jaririn kulawar gaggawa amma a ƙarshe ya ce ga garinku nan.

Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris.
Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba.
Wata majiya ta ce uwar jaririn mai shekaru 18 ta jefo shi ne ta tagar ɗakin wani otel daga hawa na biyu a Kudancin Faransa.
An bai wa jaririn kulawar gaggawa amma a ƙarshe ya ce ga garinku nan kamar yadda majiyar ta tabbatar.

’Yan sanda sun ce jaririn ya mutu da misalin ƙarfe 7:45 na safiya agogon GMT a Asibitin Debre kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito.

Bayanai sun ce uwar jaririn wadda ɗaliba ce ’yar asalin ƙasar Amurka ta jefo jaririn ne bayan haihuwarsa a ɗakin da ke hawa na biyu na otel ɗin

Tuni dai mahukunta a Faransa suka ƙaddamar da bincike kan lamarin yayin da suka tabbatar da cafke matashiyar da ake zargi.

An ruwaito cewa BaAmurkiyar na daga cikin tawagar wasu matasan ɗalibai da ke yawon ƙaro ilimi a nahiyar Turai.

A halin yanzu dai an kai matashiyar asibiti domin samun kulawar da ta dace a sanadiyar haihuwar da ta yi a yayin da bincike zai ci gaba da gudana.

 

AFP