✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Usain Bolt zai yi wa Manchester United kwallo

Zakaran tseren duniya Usain Bolt yana daga cikin ’yan kwallon da za su yi wa kulob din Manchester United na Ingila kwallo a wani wasan…

Zakaran tseren duniya Usain Bolt yana daga cikin ’yan kwallon da za su yi wa kulob din Manchester United na Ingila kwallo a wani wasan sada zumunta da kulob din zai yi da na FC Barcelona a ranar 2 ga watan Satumbar wannan shekara.

Usain Bolt dai zai hadu da tsofaffin ’yan kwallon Manchester United ne irin su Ryan Giggs da Paul Scholes da wasu a yayin wasan kamar yadda shi ma kulob din FC Barcelona zai gabatar da tsofaffin ’yan kwallonsa. Wasan zai gudana ne a filin wasa na Manchester United da ake kira Old Trafford da ke Ingila.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta The Sun ta kalato Bolt ya dade yana sha’awar ganin ya buga wa kulob din Manchester United kwallo idan ya yi ritaya  don yanzu da ya yi ritaya ne kulob din ya cika masa burinsa inda ya gayyace shi don ya yi wa kulob din kwallo. 

Bolt ya ce zai yi atisaye da kulob din Borussia Dortmund na Jamus kafin wasan, ya ce ya dade yana sha’awar wasan kwallon kafa, kuma kulob din Manchester United ne kulob din da ya fi kauna.

Bolta dai ya sha kai wa kulob din Manchester ziyara tun lokacin da Koci Aled Ferguson yake horarwa kuma ya sha yin atisaye da ’yan wasan kulob din a shekarun baya.

Usain Bolt a makon jiya ne ya yi ritaya daga tsere, bayan an kammala gasar guje-guje da tsalle-tsalle da ta gudana a Ingila.

A gasar Usain Bolt ya sha kashi ne a tseren mita na 100 da kuma na 200 da hakan ta sa ya kawo karshen shekaru 10 da ya yi yana jan ragamar gasar tsere ta duniya.