Mai yiwuwa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta maye gurbin kocinta, Ole Gunnar Solskjaer da kocin kungiyar Leicester City, Brendan Rodgers.
Wasu rahotanni da kawo yanzu ba su da wani tabbaci a hukumance, sun ce kocin Leicester City ya cimma yarjejeniyar baka da Manchester United domin maye gurbin Solskjaer saboda rashin katabus.
- Dan sanda ya kashe abokan aikinsa 4 a Indiya
- ‘Mutanen da ke fuskantar barazanar yunwa a duniya sun kai miliyan 45’
A halin yanzu dai matsayin Solskjaer na ci gaba da jagorancin horas da ’yan wasa a kungiyar ta Old Trafford na cike da rashin tabbas, la’akari da rashin nasarar da kungiyar ta yi a karawarta da Manchester City a karshen makon da ya gabata.
A ranar Asabar da ta gabata ce Manchester City wacce ta je bakunta ta lallasa United da ci 2-0 a gasar Firimiya, yayin da kuma makonni biyu da suka gabata, Liverpool ta lallasa United din da kwallaye 5-0.
Wannan kwan-gaba kwan-baya da Manchester United ke fuskanta ya sanya manyan jami’an kungiyar nazarin sallamar kocinsu, inda rahotanni suka ce tuni har sun soma tattaunawa da Rodgers na Leicester City.
Sai wasu rahotanni sun nuna duk da cewa United na son daukar Rodgers a yanzu, a bangarensa abin da yake so shi ne a jira har zuwa karshen kakar wasa ta bana.