dan kwallon tsakiya a kulob din Manchester United, Bastian Schweinsteiger ya ce kulob din yana bukatar ’yan kwallon gaba irin su Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo ko kuma Thomas Muller muddin suna bukatar zura kwallaye a raga a koyaushe
dan kwallon ya yi wannan furuci ne a karshen makon jiya jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin United da West Ham a gasar Firimiya ta Ingila, inda aka tashi wasan babu ci. Wannan shi ne karo na biyar da United take yin canjaras a cikin wasanni tara da ta yi a kakar wasa ta bana.
Wayne Ronney, dan kwallon gaba a kulob din United ne yake kan gaba wajen zura kwallaye a raga a kulob din. Kawo yanzu ya zura kwallaye bakwai ne a wasanni 20 da ya yi a kakar wasa ta bana.
Schweinteiger ya ce “A duk wasa mukan barar da kwallaye babu kakkautawa kuma hakan ce take sa da kyar muke iya samun nasara a wasa. Saboda haka muna bukatar kwararrun ’yan kwallo irin su Messi ko Ronaldo ko kuma Muller da za su taimaka mana wajen zura kwallaye a raga ba tare da matsala ba.”
dan kwallon dai yana yi wa kulob din shagube ne wajen ganin an cefano zaratan ’yan kwallon gaba a kulob din idan aka bude kakar saye da sayar da ’yan kwallo a wata mai zuwa.
United tana bukatar Messi, Ronaldo ko Thomas Muller– Schweinsteiger
dan kwallon tsakiya a kulob din Manchester United, Bastian Schweinsteiger ya ce kulob din yana bukatar ’yan kwallon gaba irin su Lionel Messi ko Cristiano…