✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

United ta kammala sayen dan bayan Madrid Raphael Varane

Dan wasan ya shafe shekara 10 a Madrid, sannan ya lashe kofi 18.

Manchester United ta tabbatar da sayen dan wasan baya na Real Madrid, Raphael Varane.

Real Madrid ta tabbatar da sayar da dan wasan, amma ba ta bayar da bayani game da yadda kasuwancin dan wasan ya kasance tsakaninta da Manchester United ba.

  1. Wata mata ta gano macizai 18 a kasan gadonta
  2. Rahoton Sahara Reporters ya fusata dubban Musulmi

Wannan zai kasance shi ne karo na biyu da Madrid din ta sayar da dan wasanta na baya a bana, bayan barin kungiyar da Sergio Ramos ya yi zuwa PSG.

Sai dai rahotanni da ke fitowa daga Ingila sun bayyana Manchester ta sayi dan wasan kan kudi Euro miliyan 50.

Tun bayan kammala gasar Euro 2020 aka fara rade-radin cewar dan wasan zai bar Madrid bayan shafe shekara 10, inda ya lashe kofi 18 ciki har gasar Zakarun Turai guda hudu.

Real Madrid, ta bayyana godiyarta ga Varane da iyalinsa kan irin gudunmawar da ya bata tsawon shekarun da ya shafe yana murza leda a kungiyar.