✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kisan Ummita: Rashin Lauya Ya Hana Gurfanar da Dan China A Kotu

Mista Geng ya nemi kotun ta dage shari'ar don ya sami yin magana da lauyansa

Babbar Kotun Jihar Kano ta sanya ranar 4 ga watan Oktoba don gurfanar da dan kasar China nan, Geng Quangrong, bisa zargin kisan budurwarsa, Ummmulkulsum Buhari, wacce aka fi sani da Ummita.

Yayin da aka gabatar da kes din a ranar Alhamis, Mista Geng ya nemi kotun da ta dage shari’ar don ya sami damar yin magana da lauyansa wanda zai wakilce shi a gabanta.

Yayin da yake mayar da martani, Kwamishinan Sharia na Jihar Kano, Barista Musa Lawan Abdullahi, bai yi suka game da rokon na wanda ake kara ba.

A cewarsa, “Daga dukkan alamu wannan kes ba zai yiwu a yau ba, domin rashin lauyan da zai kare wanda ake kara, duba da cewa laifin da ake zargin sa da shi babban laifi ne.

“Don haka muna neman a sanya mana gajeren lokaci domin wanda ake kara ya sami damar samun lauyan da zai kare shi awannan shari’a.”

Hakan ya sa alkalin kotun, Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji, ya sanya ranar 4 ga watan Oktoba mai k amawa, don gurfanar da wanda ake zargi gabanta.