An gurfanar da wasu ’yan sanda uku kan zargin fashi da makami na Naira miliyan 322 a Jihar Kano.
Gwamnatin jihar ta gurfanar da ’yan sandan ne tare da wasu mutane uku a gaban babbar kotun jihar.
- An tsare ’yan uwan juna kan zargin kashe wani mutum
- An tsare ’yan uwan juna kan zargin kashe wani mutum
’Yan sandan da ake zargi sun hada da SP Yusuf Buba da Insfekta Rabiu Umar da kuma Insfekta Mukhtar Umar ’Yan Lilo.
Mai gabatar da kara kuma lauyar Gwamnatin jihar, Barista Aishatu Salisu, ta shaida wa kotun cewa mutanen sun yi wa wani mutum mai suna Abdulrazak Sani fashin kudi kimanin Naira miliyan 322.
Lauyar ta shaida wa alkali cewa daga bisani an dawo da Naira miliyan 228 daga cikin kudin.
“A yanzu haka saura Naira miliyan 97,” in ji ta a lokacin zaman kotun.
Sai dai wadanda ake zargin sun musanta laifin da ake tuhumar su na hadin baki wajen aikata laifi da kuma fashi da makami.
Lauyar ta shaida wa kotun cewa biyu daga cikin mutanen da ake zargi ba su zo kotun ba wato Insfekta Rabiu Umar da kuma Insfekta Mukhtar Umar ’Yan Lilo.
Ta ce ta rubuta wa hukumar ’yan sanda takarda a kan a kawo su kotu amma shiru.
Sai dai lauyan da ke kare wadanda ake kara, Barista A. U. Hajj, ya roki kotun ta shari’ar mutanen da ke zuwa kotun da na wadanda ba sa zuwa.
Alkalin kotun, Mai sharia Faruk Lawan, ya amince da bukatarsa, sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Yuli, 2024.