Bayan wata bakwai babu zaman kotu, an sake dage sauraron shari’ar dan Chinan da ake zargi da kisan budurwarsa Ummulkusum Buhari (Ummita) a Kano zuwa shekarar 2024.
A yau ne aka ci gaba da sauraren shari’ar dan kasar Chinan Mista Frank Quangrang Geng, wanda gwamnatin Kano ta gurfanar bisa zarginsa da kisan budurwarsa Ummita a jihar.
- Majalisa ta ba da umarnin a tsare Gwamnan CBN da Akanta-Janar
- ’Yan bindiga sun sumar da basaraken Abuja da duka kan rashin cikar kudin fansa
Shari’ar da da ake yi tsakanin Gwamnatin Jihar da ke dan kasar Chinan ne bayan shafe watanni bakwai ba tare da zaman shari’ar ba, saboda shari’o’in zabe.
A zaman, Lauyan Dan China Barista Muhammad Danazumi ya nemi afuwar kotun bisa rashin kawo rubutaccen bayanansa na karshe daga bangarensu, sakamakon ayyukan shari’oin zabe da suka dauke masa hankali.
“A yanzu haka na kusa kammala rubuta bayanaina na karshe, zuwa makon gobe zan kammala sannan in mika wa bangaren masu kara,” kamar yadda ya shaida wa kotu.
Sai dai lauyan gwamnati, Barista Aisha Mahmud, ta yi suka game da wannan bayani na bangaren wadanda ake kara.
Amma ta ce babu yadda za su yi, “Yanzu dole sai mun jira sun kammala rubuta bayanansu na karshe sannan mu kuma mu bayar da amsa. Daga karshe kuma sai a yanke hukunci,” in ji ta.
Ta kuma nemi kotu da ta ja hankalin lauyan wanda ake kara da su mayar da hankali kan shari’ar duba da yanayin kes din wanda ya shafi kisan kai.
Alkalin kotun, Mai Shari’a, Sanusi Ado Ma’aji, ya dage shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Janairu 2024.