✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Umarni 14 da sabon Gwamnan Kano ya bayar bayan rantsar da shi

Ga muhimman umarni 14 da sabon Gwamnan ya bayar

A ranar Litinin aka rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin sabon Gwamnan Jihar Kano.

Abba dai ya karbi ragamar Jihar ce daga magajinsa, Abdullahi Umar Ganduje, kuma bikin ya gudana ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.

Aminiya ta yi nazarin jawabin da sabon Gwamnan ya gabatar jim kadan bayan rantsar da shi, inda ta tsakuro muku muhimman matakai 14 da jawabin ya mayar da hankali.

  • Za a sake dawo da shari’ar da ake yi wa Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, wanda ake zargi da kashe mutane da kuma kone wasu da ransu lokacin zabukan da suka gabata.
  • An umarci jami’an tsaro su kwace duk wata kadarar gwamnati da aka sayar ba bisa ka’ida ba.
  • An kori dukkan masu rike da mukaman siyasa a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Kano.
  • Ya kafa kwamitin kar-ta-kwana da zai yaki da masu kwacen waya da sauran laifuffukan da suka addabi.
  • Za a dawo da auren zawarawa
  • Za a binciki dukkan rikice-rikicen siyasar da aka yi a Jihar Kano tun daga shekara ta 2015 har zuwa yanzu.
  • Za a bincika fitaccen mai ra’ayin Kwankwasiyyar nan, Dadiyata, wanda ake zargin jami’an tsaro sun yi awon gaba da shi sama da shekara biyar da suka gabata.
  • Za a dawo da dogayen motocin da suke jigilar dalibai mata a Jihar, ta hanyar kwato wadanda aka sayar da kuma sayen sababbi.
  • Za a dawo da ciyar da ’yan makaranta a makarantun firamare da ke fadin Jihar.
  • Za a dawo da bayar da tallafin karo karatu a gida da ketare ga dalibai masu hazaka.
  • Za a sake bude dukkan makarantu na musamman da Kwankwaso ya gina amma aka rufe zamanin mulkin Ganduje.
  • Tsarin haihuwar mata kyauta zai dawo.
  • Dukkan masu kananan sana’o’in da jarinsu bai wuce dubu 30 ba za su daina biyan haraji.
  • Za a fito da tsarin da zai hana dillalai da masu sana’ar filaye yin ‘awon igiya’.