✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Uku daga cikin ’yan fashin da suka addabi Zariya sun shiga hannu

Dubunsu ta cika kwana daya bayan artabunsu da ’yan sanda

’Yan sanda a yankin Kasuwar Mata da ke Sabon Garin Zariya a Jihar Kaduna sun cafke uku daga cikin ’yan fashin da suka addabi yankin.

An kama su ne yayin wani farmaki da suka kai bayan samun rahoton ta’adin da suka yi a Anguwar Jaba.

Bayanan da Aminiya ta tattara kan ta’adin da ’yan fashi suka yi na shiga gidajen jama’a a daren Juma’a zuwa safiyar Asabar, ya sanya tawagar ‘yan sanda a karkashin babban jami’in yankin suka kutsa cikin dajin da ’yan fashin suka bi domin kamo su.

Hakarsu ta cim ma ruwa inda suka samu galaba a kan ’yan fashin, inda suka harbi mutum biyu amma suka gudu da raunin harbi a jikinsu.

Kazalika, sun kuma kwato babura guda biyu da wayar hannu guda shida.

Tawagar ’yan sandan ba su yi kasa a gwiwa ba, da gari ya waye sai suka koma wajen da suka yi artabu da ’yan fashin, inda suka bi jinin da ya zuba kuma suka bi har suka kai kofar dakin da ya tsaya, inda a ciki ne suka samu mutane ukun.

Hakan ne ya tabbatar da cewa suna daga cikin tawagar ’yan fashin kuma daya daga cikin wadanda aka harba ya mutu kuma sun jefa shi a ruwa yayin da dayan an tafi domin yi masa magani.

’Yan fashin da yawansu ya kai kimanin 30 sun addabi mazauna yankin kimanin makonni biyu ke nan.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce ana ci gaba da bincike don gano sauran wadanda suka gudu domin su fuskanci shari’a.

%d bloggers like this: