✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ukraine ta yi wa Putin sabon tayin sulhu

Zelensky ya ce Ukraine ba za ta mika wuya ba sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi

Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce kasarsa ba za ta mika wuya ga Rasha ba, har ta ga abin da zai ture wa buzu nadi a yakin da ke tsakaninsu.

Zelensky ya yi kwaskwarima ga batun tattaunawarsa gaba-da-gaba da Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, cewa za su yi muhawara, har ma da batun zaben raba-gardama a kan matsayin yankunnan Donetsk da Luhansk da ke neman ballewa daga Ukraine.

Ya shaida wa kafafen yada labarai a kasarsa a daren Litinin cewa “A shirye nake da in dauko wadannan batutuwa a tattaunawarmu ta farko da Shugaban Kasar Rasha.”

Ya bayyana cewa batutuwan da zai gana da Putin a kai sun hada har da matsayin yankin Donbas da ya balle daga Ukraine yake kuma samun goyon bayan Rasha, da kuma yankin Crimea na kasarsa da Rasha ta mamaye.

A cewarsa, a shirye yake ya tattauna da Putin “ta kowace fuska” domin ganin an kawo karshen yakin da aka shafe kusan wata guda ana yi, wanda kuma ya ruguza al’amura a Ukraine.

“Babu wani batun lallashi ko dogon surutu. Za mu yi zuzzurfar tattaunawa ne da shi a kan duk wadannan batutuwa,” inji shi.

Masu neman ballewa

Rasha ta ayyana Crimea a matsayin yankin kasarta, sannan take daukar yankunan Donetsk da Luhansk da ke  Gabashin Ukraine da suke neman ballewa a matsayin kasashe masu ’yancin kansu.

Yankunan uku dai sun kasance ne a cikin kasar Ukraine, tun bayan rushewar tsohuwar Tarayyar Soviet.

Kimanin shekara 10 ke nan Rasha da Ukraine suke takaddama a kan yankunan, har ta kai ga mamayar da Rasha ta auka wa Ukraine da yaki a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2022.

Shin za a daidaita?

“Idan har na samu dama kuma Rasha ta ga dama za mu tattauna wadanna abubuwa domin ganin an warware su.

“Sai dai kuma, shin za mu iya warware su gaba daya? A’a. Amma akwai yiwuwar warware wadansu daga cikinsu – akalla dai a dakatar da yakin,” inji Zelensky.

Amma duk da cewa ya nuna cewa yana son su tattauna a kan makomar yankunan uku, shugaban na Ukraine yana kan bakarsa na cewa yankunan kasarsa ne kuma kasar ba za ta hakura da su ba.

Ya kara da cewa duk wani sauyi da zai taba tarihi, to dole sai an yi zaben raba-gardama a kansa.

Me zai faru?

Wata kwararriya a kan kasar Ukraine daga Jami’ar Australia, Sonia Mycak, ta ce batun zaben raba-gardama tamkar cewa ne Ukraine ba za ta sallama wani yanki daga cikin kasarta ba.

Ta bayyana cewa, “Akalla kashi 80 cikin 100 na ’yan Ukraine ba sa son a sallama yankunan,” kamar yadda zaben jin ra’ayoyin jama’a ya nuna sau biyu a baya-bayan nan.

Ta ce, “Bisa dukkan alamu ’yan kasar za su yi watsi da ficewar yankunan domin yawancin mutanen Ukraine cewa suke ‘kar mu daina yakin’, saboda a ganinsu, dorewar kasarsu na fuskantar barazana.

“Domin ba wai yankunan kawai za su rasa, a’a, za su ci gaba da zama ne a matsayin ’yan Rasha, karkashin ikon Rasha da kuma kama-karya.”

Ta ki ci, ta ki cinyewa

Kusan wata guda ke nan ana tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatocin Rasha da Ukraine ba tare da an cimma matsaya ba kan rikicin da ya tilasta akalla mutum miliyan 3.5 tserewa daga Ukraine.

Bisa alamu dai, duk da karfin sojin Rasha – da kuma yadda ta gagara mamaye daukacin Ukraine kawo yanzu – Gwamnatin Zelensky da ke samun goyon bayan al’ummar  Ukraine na ganin za a iya yi wa tufkar hanci a kan teburin sulhu.

Da yake magana game da Putin, Mista Zelensky ya ce, “Babu yadda za a yi a ce babu mafita. Idan [Putin] ya lalata kasarmu, kansa yake lalatawa.

“Ba na son a yi ta komawa tarihi a matsayinmu na jarumai da kuma kasar da babu ita…. Idan har suka rusa kansu, to babu sauran jarumtar da ta rage musu.”