✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ukraine ta yi fatali da tayin Rasha na tattaunawa a Belarus

Ukraine ta ce a shirye take ta tattauna da Rasha, amma ba a kasar ta Belarus ba.

Kasar Ukraine ta yi watsi da tayin da Rasha ta yi mata na hawa teburin sulhu da ita a kasar Belarus.

Matakin na zuwa ne yayin da Rashar ta shiga yini na hudu da kaddamar da hare-hare a kan kasar ta Ukraine.

Shugaban Kasar ta Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya ce kasarsa a shirye take ta tattauna da Rasha, amma ba a kasar ta Belarus ba, wacce suke yi wa kallon ’yar kanzagin Rashar.

Kalaman na Shugaba Volodymyr na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Rasha ta ce tawagarta a shirye take ta hadu da ta gwamnatin Ukraine domin tattaunawa a birnin Gomel na kasar Belarus.

Rasha dai ta girke dubban dakaru a kasar ta Belarus tun ma kafin ta kai ga mamaye kasar ta Ukraine, inda Ukraine din ta zargeta da yin amfani da Belarus din a matsayin sansanin kaddamar mata da hare-hare.

Tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewa dakarun na Rasha sun shiga Kharkiv, birnin na biyu mafi girma a Ukraine, a kokarinsu na danganawa da Kyiv, babban birnin kasar.