A yayin da aka fara hawa teburin sulhu kan rikicin kasashen Rasha da Ukraine a kan iyakar kasar Belarus ranar Litinin, Ukraine ta nemi a tsagaita wuta.
Rahotanni sun ce kowace daga cikin kasashen biyu dai ta ja daga a tattaunawar da aka fara, inda kowace ta jero bukatunta, muddin ana so sulhun ya kai ga nasara.
- Kotu ta ki amincewa ta bayar da belin Abba Kyari
- Sarakunan Kano da Katsina sun sa labule kan murabus din Wazirin Katsina
Gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya bukaci sojojin Ukraine su hambarar da gwamnatin shugaba Volodymyr Zelenskyy, saboda ya ce haramtacciya ce.
Shi kuwa a nasa bangaren, Ministan Harkokin Waje na Rasha, Sergey Lavrov, ya ce ba su amince da gwamnatin Ukraine a matsayin halastacciya ba, duk da cewa Shugaban Kasar ya lashe zabe da kaso 73 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben kasar na 2019.
Yanzu haka dai ana ci gaba da fafatawa duk kuwa da tattaunawar da ake ci gaba da yi, lamarin da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum ke cewa yana da wuya a kai ga tsagaita wutar cikin kankanin lokaci.
Ya zuwa safiyar Litinin dai, adadin yawan fararen hular da aka kashe a rikicin ya kai 352, ciki har da kananan yara 14, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Ukraine ta sanar.