Shugaban Ukraine Volodymyr Zelinsky ya ce ya amince zai yi zaman sulhu da Rasha a wani wuri kan iyakar Ukraine da Belarus.
Mista Zelensky ya ce a tattaunawar da ya yi da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, Ukraine ta amince ta gana da Rasha ba tare da wani sharadi ba a kan iyakar Ukraine da Belarus a kusa da kogin Pripyat.
- Leeds United ta raba gari da kocinta Marcelo Bielsa
- Ukraine ta yi ikirarin hallaka dakarun Rasha 4,300
Shugaban Ukraine ya ce Mista Lukashenko ya ce ya dauki alhakin tabbatar da dakatar da shawagin dukkanin jiragen sama, masu saukar angulu da masu kakkabo makamai mai linzami lokacin ziyarar domin tattaunawar tsakanin bangarorin biyu.
Aminiya ta ruwaito cewa tun da farko ne dai kasar Ukraine ta yi watsi da tayin da Rasha ta yi mata na hawa teburin sulhu da ita a kasar Belarus, inda shugaba Zelensky ya ce ya fi bukatar a tattauna a wata kasar sabanin Belarus.
Bayanai sun ce Belarus babbar aminiyar Rasha ce a yakin da take da Ukraine, wacce ake yi wa kallon ’yar kanzagin Rashar.
A ranar Lahadi ce Rasha ta sanar cewa ta tura wakilai Belarus domin tattaunawa da jami’an Ukraine.
Matakin watsi da tayin na zuwa ne yayin da Rashar ta shiga yini na hudu da kaddamar da hare-hare a kan kasar ta Ukraine.
Rahotanni sun ce kalaman na Shugaba Volodymyr na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Rasha ta ce tawagarta a shirye take ta hadu da ta gwamnatin Ukraine domin tattaunawa a birnin Gomel na kasar Belarus.
Rasha dai ta girke dubban dakaru a kasar ta Belarus tun ma kafin ta kai ga mamaye kasar ta Ukraine, inda Ukraine din ta zargeta da yin amfani da Belarus din a matsayin sansanin kaddamar mata da hare-hare.
Tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewa dakarun na Rasha sun shiga Kharkiv, birnin na biyu mafi girma a Ukraine, a kokarinsu na danganawa da Kyiv, babban birnin kasar.