Manchester United ta rike Atletico Madrid har gida inda aka tashi kowa na da kwallo daya a ragarsa, yayin da Benfica da Ajax suka tashi 2-2.
A daren ranar Laraba ne a ci gaba da gasar gasar Zakarun Turai, inda Atletico Madrid ta karbi bakuncin Manchester United, Benfica kuma ta karbi bakuncin Ajax.
- Karin kudin tikitin jirgin sama ya jawo karancin fasinjoji
- Fina-finan Nollywood ke haddasa kisa don tsafi a Najeriya —Lai Mohammed
An buga wasan Atletico Madrid da Manchester United ne a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid a kasar Spain.
Dan wasan gaban Atletico Madrid, Joao Felix ne ya fara zuwa kwallo a minti na bakwai da fara wasa, sai kuma dan wasan Manchester United Anthony Elanga ya warware kwallon a minti na 80.
A karawar Benfica da Ajax kuwa leda aka murza mai ban sha’awa a filin wasa na Estadio da Luz da ke kasar Portugal.
Dan wasan Ajax Tadic ne ya fara cin kwallo a minti na 18, daga baya kuma Haller, wato dan wasan gaban Ajax ya zura kwallo a ragar kungiyarsa (own goal) a minti na 26.
A minti na 29 Haller ya kara kwallo ta biyu a ragar Benfica, sai kuma Yaremchuk ya zare kwallon a minti na 72.
Haka aka tashi duka wasannin biyu, wato kowa na nema; Za a dawo zagaye na biyu na wasan a ranar 15 ga watan Maris, 2022.