A wannan makon za mu yi bincike ne a kan jarabobi da muke fuskanta a cikin rayuwan mu na yau da kulum. A takaice dai babu wani mai rai da zai ce bai taba fuskantar jarabobi a rayuwar sa ba. Jarabobi na zuwa mana ne ta hanyoyi daban-daban; yakan iya zama ta bangaren rashin lafiya, dukiya, wurin aiki, iyali, da dai makamantan su. Abin tambaya a nan shi ne, jarabobi na zuwa ga wanda yayi zunubi ne kadai? Bari muga ansar mu a cikin littafi mai tsarki.
Ayuba 1:1-31, 6 -12; Akwai wani mutum a ?asar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ?in aikata kowace irin mugunta. Yana da ‘ya’ya bakwai maza, uku mata. Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da ra?uma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ?ari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ?asar gabas arziki nesa. 6 – 12 Sa’ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta yi, Shai?an ma ya zo tare da su. Sai Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Kai fa me kake yi?” Shai?an ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, a ko’ina a duniya.” Ubangiji ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ?in aikata kowace irin mugunta.” Shai?an ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maka sujada? Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ?asan nan. Amma da a ce za ka raba shi da dukan abin hannunsa, to, da zai fito fili ya zage ka ?iri ?iri.” Ubangiji ya ce wa Shai?an, “To, shi ke nan, dukan abin hannunsa yana cikin ikonka, amma shi kansa kada ka cuce shi.” Sai Shai?an ya tafi.
A nan mun ga cewa Ayuba mutum ne mai tsoron Allah, natsattse, mai kin kowace irin mugunta yana kuma da arziki mai yawa, amma me ya faru? A aya ta 6 zuwa 12 mun ga cewa Allah ya ba wa Shai?an daman jarabtan Ayuba. Abin lura a nan shi ne, duk jarabobi da muke fuskanta a cikin rayuwan mu, Allah na sane da su, kada kuma mu ga cewa ai Allah baya kaunarmu ba, sam, sam. Allah ne ya halicce mu, Shi ya bamu rai, Yana kuma da iko bisan mu. So da dama zaka ga mutane a cikin rashin sani idan abu ya faru da su misali a ce mutuwan uba, uwa ko da, ko kuma mu ce dukiyan su ya kone ta wurin hadarin wuta, zaka ga suna kuka suna tambaya me ya sa Allah ya bar abu haka ya faru da su? A ganin ka abin da ya kamata su yi ko kuma su fadi ke nan a irin wannan lokaci? Babu shakka irin wannan yanayi na da matukan zafi a zuci amma Ubangiji Allah ya ce mana a littafin 1 Korantiyawa 10:13 “Ba wani gwajin da ya ta?a samunku, wanda ba a saba yi wa ?an adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ?arfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi”. Tabbacin yana da sanen duk matsalolin da muke ciki Ya kuma bamu abin da zai taimake mu a irin wannan lokuta, wato maganar Sa da sanin Sa. Sanin Ubangiji kadai zai sa mu gane kowace irin yanayi da muka fada ciki. Ishaya 41:13 “Ni ne Ubangiji Allahnku, Na ?arfafa ku, na kuwa fa?a muku, ‘Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku”, Filibiyawa 4:6-8 “Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da ro?o, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu”, Zabura 50:15; “Ku yi kira gare ni sa’ad da wahala ta zo, Zan cece ku, ku kuwa za ku yabe ni.”
Bari mu dauki Jarabobi a matsayin matakala ne na rayuwa ga sanin Ubangiji, a duk lokacin da muka shiga irin wannan yanayin. Shi ya sa ya kamata mu san littafi mai tsarki, mu na yin bincike muna nazari da kuma adu’a dare da rana ba tare da sai wani ya fada mana me ke cikin ta ba. Domin rayuwa na nan ne kamar makaranta, a karshen ko wace darasi malami yakan ba da jarabawa don ya gwada dalibansa ko sun fahimci abin da suka koya. Wanda ya ci nasara akan bashi lambar yabo, sanan wanda ya fadi yakan maimata darasin ko ya sami lambar faduwa, hakannan rayuwa ta ke. Sai mu yi lura mu yi koyi da kowace irin jarabobi da mu ke fuskanta a rayuwan mu, muna rokon Ubangiji muna kuma gode maSa a kowace yanayin da muka sami kan mu a ciki.
Yakubu 1:2-4 “Ya ku ‘yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ?warai. Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri. Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba”.
Ubangiji Allah Ya taimakemu, amin.