“Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, Shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.” Karin Magana 3:5-6
Barkanmu da sake haduwa a wannan sabuwar shekara ta 2018. Godiya da daukaka da girma sun tabbata ga Ubangiji Allah Mai iko duka da Ya bar mu cikin masu rai. Ta wurin alherinSa ne muka iya ganin shekara ta 2018 da kuma ranar yau, ba da ikon kanmu ba ne ko iyawarmu da illiminmu ba, amma domin kaunarSa mafi girma zuwa gare mu ta wurin Yesu Almasihu.
A wannan sabuwar shekara, mece ce madogararka?
Shekarar da ta shige 2017, mutane da yawa sun yi ta shirin shiga wannan sabuwar shekara ta 2018, wadansu sun yi ta tattalin kudi, wadansu abinci da gidaje da makamantansu, duk da haka da yawa daga cikinsu ba su ga sabuwar shekarar ba. Idan haka ne, me ya kamata mu yi a wannan sabuwar shekara domin sabunta rayuwarmu? A wannan shekara ta 2018, akwai kwananki 365 da yardar Ubangiji, wato kana da zarafi guda 365 na sanin ikon Ubangiji cikin rayuwarka. Kowace rana na dauke da albarkokinSa, Shi kadai ne kuma Ya san me kowace rana ke tafe da shi, Shi ne farko da kuma karshen komai da kowa. To, idan kana sane da wannan, a wannan sabuwar shekara ya kamata ka bidi fuskar Ubangiji a koyaushe, kowace rana da zuciya daya don neman jagorancin Ubangiji. Ba da ikon kanka ba ne za ka ci nasara a wannan rayuwa, amma sai dai ikon Ubangiji kadai. Idan muka ci gaba da karatunmu cikin Littafin Karin Magana 3:7-8 za mu ga cewa:: “Sam, kada ka yarda ka dauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta. Idan ka kiyaye wannan, zai zama maka kamar magani mai kyau, ya warkar da raunukanka, ya kuma sawwake maka azabar da kake sha. A cikin duk abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji.” To, hakan nan rayuwarka take a wannan sabuwar shekara? Kana bidar fuskar Ubangiji ka kuma dogara gare Shi da zuciya daya a kowace rana da kuma duk abin da kake yi ko cikin wani hali da ka tarar da kanka a ciki? Idan fa ba haka ba, sai ka fara tun yanzu domin ka mori albarkatun Ubangiji a wannan sabuwar shekara.
Kamar yadda Ubangiji Ya gaya wa Joshua “Ashe, ban umarce ka ba? Ka dage ka yi karfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka Yana tare da kai duk inda za ka.” (Joshua 1:9). Haka Ubangiji zai ba mu karfin hali Ya kuma kasance tare da mu a duk inda za mu shiga a wannan shekara idan muka dogara gare Shi, haka kuma albarkokin Ubangiji za su kasance tare da kai idan ka dogara ga Ubangiji. Irmiya 17:7-8, “Mai albarka ne mutumin da ke dogara ga Ubangiji, Wanda Ubangiji ne madogararsa. Shi kamar itace ne wanda aka dasa a bakin rafi Wanda ke mika saiwoyinsa zuwa cikin rafin, Ba zai ji tsoron rani ba, Kullum ganyensa kore ne, Ba zai damu a lokacin fari ba, Ba zai ko fasa yin ’ya’ya ba.”
Bari mu rufe bincikenmu na wannan makon da Zabura 91, “Zama a inuwar Mai iko duka. Duk wanda ya je wurin Madaukaki zai zauna lafiya. Duk wanda yake zaune a inuwar Mai iko duka, ya iya ce wa Ubangiji, “Kai ne kariyata, kuma mai kiyaye ni! Kai ne Allahna, a gare Ka nake dogara!” Hakika zai kiyaye ka daga dukan hadarurruka da ke boye, Daga kuma dukan mugayen cututtuka. Zai rufe ka da fika-fikansa, Za ka zauna lafiya a karkashinsu. AmincinSa zai tsare ka, ya kiyaye ka. Ba za ka ji tsoron hadarurrukan dare ba, Ko fadawar da za a yi maka da rana, Ko annobar da take aukowa da dare, Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana. Mutum dubu za su fadi daura da kai, Dubu goma kuma za su fadi dama da kai, Amma kai, ba za a cuce ka ba. Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye. Domin ka dauka Ubangiji Yake kiyaye ka, Madaukaki ne Yake tsaronka, To, ba bala’in da zai same ka, Ba za a yi wa gidanka aikin karfi da yaji ba. Allah zai sa mala’ikunSa su lura da kai, Za su kiyaye ka duk inda za ka tafi. Za su dauke ka a hannuwansu, Don kada ka buga kafarka a dutse. Za ka tattake zakuna da macizai, Za ka tattake zakuna masu zafin rai Da macizai masu dafi. Allah Ya ce, “Zan ceci wadanda suke kaunaTa, Zan kiyaye wadanda suka san Ni. Sa’ad da suka yi kira gare Ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa’ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su. Zan ba su tsawon rai da lada, Hakika kuwa zan cece su.”
Ubangiji Allah Ya kai mu mako mai zuwa, amin.