Mahaifin wata yarinya ya lakada wa wani likita dukan tsiya kan mutuwar ’yar tasa mai data 15 a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Abekuta, a Jihar Ogun.
Mahaifin yarinyar ya zargi ma’aikatan lafiyar asinitin da kin ba wa ’yarsa kulawar da ya kamata, wanda a tunaninsa haka ne ya yi sanadin ajalinta.
- Yadda kananan yara suka rasu yayin wasa a cikin fada
- Masu garkuwa da daliban jami’a mata na neman N50m
- An kashe ‘yan bindiga 9 tare da kame wasu a Jihar Neja
- ’Yan bindiga sun kai hari makarantar firmare, sun sace dalibai
Jami’in Hulda da Jama’a na asibitin, Segun Orisajo, ya bayyana yadda magidancin ya yi ta amfani da kujerar katako yana dukan likitan bayan samun labarin rasuwar yarinyar.
Sai dai Orisjo bai bayyana sunan mahaifin yarinyar ko likitan da aka yi dukan ba.
A cewarsa, jaririyar ta yi mfama da zazzabi har na tsawon wata guda, ja kuma rama da rashin kula, yayin da rashin lafiyar ta yi tsanani.
“Bayan iyayen yarinyar sun ce ba su da kudi, sai aka dauke musu kudin gwaji da sauran magnguna.
“Da misalin karfe 12 na dare ta rasu, sa’o’i hudu bayan kwantar da ita a cibiyar.
“Amma mahaifinta ya shiga dukan masu kula da ita, yana ganin sun yi jinkiri wurin ba ta kulawa.
“Da ya fusata, sai ya kama dukan likitan a kai, har sai da mutane suka kawo masa dauki.
Orisajo ya bayyana yadda daraktan cibiyar Farfesa Adewale Musa olomu, ya tausaya wa iyayen yarinyar kan rasuwar da ta yi.
“Ya kamata iyaye su fahimci cewar ajiye yaro a gida yana fama da matsanancin ciwo har na tsawon wata guda ganganci ne.
“Tabbas, yi mun kokarin ceto rayuwarta, da tun da wuri aka kawo ta da wani labarin ake yi ba wannan ba a yanzu,” a cewarsa.
Musa Olomu ya bayyana dukan da aka yi wa likitan a matsayin karo na hudu da ake dukan ma’akatansu kan wani abu idan ya faru.
Sai dai ya yi gargadi kan cewa, ba za su ci gaba da lamuntar hakan na faruwa ba, domin na gaba to kotu ce za ta raba su.