✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Uba ya karya hannun jaririnsa mai wata 2 saboda kuka

Dukan kawo wukan ya karya hannun jaririn tare da yi masa mummunan rauni sai da aka yanke hannun

Wani magidanci ya lakada wa jaririn dansa mai wata biyu da haihuwa duka, har ya karya masa hannu saboda ya hana shi barci.

Dukan kawo wukan ya karya hannun daman jaririn tare da yi masa mummunan rauni wadanda suka yi sanadiyar yanke hannun a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Owerri, Jihar Imo.

Magidancin ya yi amfani da hangar rataye kaya ne ya rika jibgar jaririn, saboda kukan da yake tsalawa ya hana shi barci.

Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa (NHRC) tabukaci Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Imo ta cafke mutumin, da ya yi jaririnsa mai wata biyu da haihuwa wannan aika-aika.

Hukumar ta yi kiran ne tare da da kungiyar Mata Yan Jarida (NAWOJ) da mahaifar jaririn, suna masu neman a kwato masa hakkinsa daga wannan rashin imani da mahaifinsa ya nuna masa.

Shugabar NAWOJ Reshen Jihar Iko, Dokta Dorothy Nnaji wadda ta ziyarci jaririn da mai jegon a asibiti ta ce shekarun mahaifin yaron 31 kuma dan asalin kauyen Amiril da ka Karamar Hukumar Isu ta jihar ne.