✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uba ya ɗaure ɗansa tsawon kwanaki uku babu abinci a Bauchi

Mahaifin ya ɗaure yaron ne a dalilin satar kayayyaki da yake yi wa wani maƙwabcinsu.

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta ce ta kuɓutar da wani yaro ɗan shekara biyar da aka ce mahaifinsa ya ɗaure shi da sarƙa tsawon kwanaki uku babu abinci a unguwar Gwallagan Mayaka da ke jihar.

An samu rahoton maƙwabtan mahaifin mai suna Abubakar Nuhu wanda aka fi sani da Wanzam sun sanar da ‘yan sanda bayan sun gano yaron a ɗaure.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Juma’a.

SP Wakil ya bayyana cewa tun a ranar Laraba Dagacin gundumar Gwallagan Mayaka ya kai wa ’yan sanda rahoton cewa ya samu labari faruwar lamarin daga wani mazaunin unguwar.

“Wani mazaunin unguwar ya bayyana cewa matarsa, Amina, ta sanar da shi cewa ta ga wani yaro ɗan shekara 5 na maƙwabtansu ɗaure da sarƙa a cikin wani ɗaki da ke gidan a unguwar.

“Nan da nan Amina ta duba yaron don tabbatar da halin da yake ciki, ta same shi kwance a sume, an ɗaure shi da sarƙa.

“A lokacin da aka karɓi bayanin, ayarin masu bincike ƙarƙashin jagorancin CSP. Mubarak S. Baba DPO D’ Diɓision, Dutsen Tanshi sun ziyarci gidan da lamarin ya faru, inda suka ceto yaron,” in ji Wakil.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, a wata hira da aka yi da shi, Hussaini, ya bayyana cewa mahaifinsa ya ɗaure shi da sarƙa ba tare da abinci ba har tsawon kwanaki uku.

Wakil ya ce, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Auwal Musa Muhammad, nan take ya umurci jami’in ‘yan sandan shiyya da a kama mahaifin yaron domin gudanar da bincike.

Ya ce wanda ake tuhumar ya yi iƙirarin cewa ya ɗaure yaron ne a dalilin satar kayayyaki da yake yi wa wani maƙwabcinsu.