Ministan Sufirin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta za ta fara ba ’yan Najeriya izinin shiga kasarta daga ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, 2020.
Hadi Sirika ya ce run ranar 30 ga watan Satumba UAE ta rubuto masa wasikar amincewar fara ba ’yan Najeriya izinin shiga daular, bayan gwamnati ta janye takunkumin da ta sanya wa jiragen Emirates.
“UAE ta rubuto cewa za ta fara ba ’yan Najeriya biza bayan mun amince jiragen Emirates su ci gaba da shigowa Najeriya”, inji shi.
Ya ce ba da izini shiga kasar zai zo da ka’idoji, saboda haka mutane su yi hakuri da abun da ba su saba gani ba.
Sirika ya ce za a ba wa matafiya tikitin jeka-ka-dawo da sakamakon PCR inshorar lafiya.
“Za a iya biyan inshorar lafiya ta hannun kamfanonin kula da matafiya ko na jiragen sama”, a cewar ministan.