✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyaftin Shehu Iyali: Tsohon mai tuƙa jirgin shugaban ƙasa ya rasu

Za a yi jana'izar Kyaftin Shehu Iyal a yau Juma'a da yamma a unguwar Ƙwarbai cikin birnin Zariya.

Kyaftin Shehu Iyali, tsohon mai tuƙa jirgin shugaban ƙasan Najeriya ya rasu.

Marigayin ya kasance mataimaki na musamman kan sufurin jiragen sama a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Kyaftin Shehu Iyal ya rasu ne a ranar Alhamis bayan ya yi fama da jinya.

Kafin rasuwarsa shi ne shugaban kamfani jiragen sama mai suna Afri Air.

Marigayin yakasance jigo a harkar sufurin jiragen sama a Najeriya kuma ya tuka shugabannin ƙasa.

A shekarar 1977 Kyafin Shehu Iyal ya kammala karatun digiri ɗinsa a Jami’ar Ahmadu Bello kafin daga bisani ya shiga Kwalejin Koyon Tuƙin Jiragen Sama (NCAT) da ke Zariya.

Kafin rasuwarsa ya riƙe muƙamai da dama a fannin sufurin jiragen sama har da Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa a matsayin mai kula da sashin zirga-zirgar jirage na hukumar.

Bayanai daga iyalan marigayin na nuni da cewa za ayi jana’izar Kyaftin Shehu Iyal a yau Juma’a da yamma a unguwar Ƙwarbai cikin birnin Zariya.