✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya a ranar 16 ga watan Janairu.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), domin halartar Taron Bunƙasa Ci Gaba Mai Ɗorewa na shekarar 2025.

Taron, wanda zai gudana daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Janairu, zai mayar da hankali kan bunƙasa ci gaba mai ɗorewa da kuma inganta ci gaban tattalin arziƙi a duniya.

Taron zai samu halartar shugabanni daga gwamnati, kasuwanci, da ƙungiyoyin al’umma don tattauna hanyoyin gina kyakkyawar makoma mai ɗorewa.

Shugaba Tinubu, ya tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Asabar.

Tinubu zai halarci taron ne bayan samun gayyata daga Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.

A yayin taron, Tinubu zai bayyana ƙoƙarin gwamnatinsa a fannonin makamashi, sufuri, kiwon lafiya, da bunƙasa tattalin arziƙi.

Ana sa ran Shugaban zai dawo Najeriya a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu.