Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta dage haramcin bayar da biza da ta kakaba wa matafiyan Najeriya.
Haramcin, wanda aka sanya watanni 10 da suka gabata, ya shafi al’amuran ‘yan Najeriya da ke zuwa Gabas ta Tsakiya don kasuwanci, yawon bude ido da kuma harkokin nishadi.
Sai dai Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin yin duk abin da zai iya domin warware takaddamar diflomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu.
Hakan na zuwa ne lokacin da Shugaba Tinubu ya gana da Ambasada Salem Saeed Al-Shamsi.
Aminiya ta ruwaito yadda Tinubu ya zarce zuwa Abu Dahbi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawan bayan ya halarci taron G-20 na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arzikin duniya a Indiya.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Cif Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa ganawar da mahukuntan UAE ta yi tasiri.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, sun kammala wata yarjejeniya, kan batutuwan da suka shafi haramcin bai wa ’yan Najeriya bizar zuwa Dubai.”
“Bugu da kari kuma, bisa wannan yarjejeniya, kamfanonin jiragen saman Etihad da na Emirates za su dawo da jadawalin tashi da saukar jiragen sama a Najeriya nan take.
“Kamar yadda shugabannin kasashen biyu suka cimma matsaya, wannan dawo da ayyukan jiragen da aka yi nan take, ta hanyar wadannan kamfanonin jiragen sama guda biyu, bai shafi wani kudi da Gwamnatin Najeriya za ta biya ba.
“A bisa la’akari da tsarin diflomasiyya na bunkasa tattalin arziki na Shugaba Tinubu, an kafa tsarin da aka amince da shi, wanda zai kunshi sabbin jarin biliyoyin dalar Amurka da dama a tattalin arzikin Najeriya a bangarori da dama, ciki har da tsaro, noma da sauransu, ta hannun gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa.
“Bugu da kari, Shugaba Tinubu ya yi farin cikin samun nasarar yin shawarwarin hadin gwiwa, sabon shirin musayar kudin waje tsakanin gwamnatocin biyu, wanda za a bayyana dalla-dalla a makonni masu zuwa.
“Tinubu ya yaba wa shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, wajen martaba matsayin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.”