Hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun dakatar da bayar da biza ga ’yan Najeriya masu son zuwa Dubai.
Sanarwar hakan na kunshe ne a wata takarda da gwamnatin kasar ta aiko wa hukumomi Najeriya da kuma masu shirya tafiye-tafiye a ranar Juma’a.
- Malamin da ya ki karbar aiki a Dubai don kishin Najeriya ya koka kan yajin aikin ASUU
- Dalilin da ’yan Najeriya ke fuskantar tsangwama a Dubai —Gwamnati
A cewar Tribune, takardar ta fito karara ta bayyana cewa “ duk wata bukatar izinin zuwa Dubai ba za a karbe ta ba”.
Sananan ta kara da cewa, “Wannan kin bayar da izinin ya shafi kowa a Najeriya.”
Lafazin takardar na nufin hatta jami’an hukumomi da kuma gwamnati, ba za a ba su bizar ba, har sai nan da wani lokaci.
Ga wadanda suka mika tarkardun bukatarsu, suka kuma biya, ba za a mayar musu da kudadensu ba, a cewar rohoton.
Wannan hanin shi ne mataki da kasar UAE ta dauka na baya-bayan nan tsakaninta da Najeriya.
Kasar ba ta kuma bayar da dalilin daukar wannan mataki kan ’yan Najeriyar ba.