Rashin damar gyara kuskuren rubutun da aka wallafa a Twitter na dab da zama tarihi.
A ranar Alhamis kakakin kamfanin Twitter, Stephanie Cortez, ta sanar cewa a watan Satumba da muke ciki masu amfani da kafar za su fara iya yin gyara ko sauye-sauye ga abin da suka riga a wallafa a shafukansu.
- An kama dan shekara 4 da bindiga makare da harsasai a makaranta
- Ma’aikaciyar Google ta ajiye aiki saboda nuna wa Falasdinawa bambanci
A baya dai masu amfani da Twitter ba sa iya gyara kuskuren rubutu ko yin kari a kan abin da suka riga suka wallafa, sabanin irinsu Facebook.
Stephanie Cortez ta ce masu amfani da babban tsarin Twitter, wato Premium Blue, su za su fara cin moriyar sabuwar damar a watan Satumba, kafin daga bisani ya kai ga kananan masu amfani da kafar.
Yadda ‘Edit’ din Twitter zai yi aiki
Stephanie Cortez ta ce korafe-korafen da suke samu ya nuna kawo yanzu babbar bukatar masu amfani da Twitter ita ce samun damar yin gyara a abin da aka wallafa a kafar.
Don haka ta ce nan gaba za a samu maballin ‘Edit’ a kafar, wanda tuni aka fara yin gwajinsa a cikin kamfanin domin tabbatar biyan mukatar masu amfani.
Sai dai ta yi karin haske da cewa, mutum zai samu damar yin ‘Edit’ ne cikin minti 30 na farko bayan ya fara wallafa sakonsa, wadanda ba zai haura haruffa 280.
A cikin wannan dan lokaci zai mutum iya gyara kuskuren rubutu ko ya sanya hashtag a kan abin da ya fara wallafawa.
Stephanie Cortez ta bayyana cewa kayyade lokacin da za a iya yin gyara na da muhimmanci domin tabbatar da armashi da ingancin batutuwan da ake tattaunawa da kuma kafa hujja da su.
Duk da haka, akwai alama ko maballi (label), wanda idan aka shiga za a ga ainihin sakon da aka fara wallafawa (da tarihin lokacin da aka wallafa) da kuma lokacin da aka yi masa kwaskwarima.
Kamfanin ya ce yana kan gudanar da bincike domin tabbatar da babu wata matsala, da kuma gano ko mutane za su iya amfani da sabuwar damar ta mummunar hanya.