Dan ta’addan nan da ya addabi yankin Zamfara da Sakkwato, Bello Turji, ya yi garkuwa da ’yan aike da suka je kai mishi Naira miliyan 10 da ya sanya wa garinsu haraji.
A ranar Talata ne Turji ya sa yaransa su yi awon gaba da biyar daga cikin mutum bakwai da suka kai mishi kudin a matsayin ‘harajin kariya,’ da ya kakaba wa wa garin Moriki da ke Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.
- Martani: Ba jiharmu ce ta fi ko’ina talauci ba a Najeriya – Sakkwato
- Dan bindiga ya harbe mutum 10 a kantin sayar da kaya a Amurka
Wani dan garin, Sani Moriki ya ce, “Da aka shida wa Turji cewa Naira miliyan 10.5 ne kudin da aka kai ba miliyan N2o da ya bukata ba sai ya fusata, ya umarci yaransa su rike biyar daga cikin ’yan sakon su tafi da su Dajin Jirari; ko da yake biyu daga cikin mutanen sun dawo gida yau da safe.”
Sani ya ce, “Yanzu muna cikin tashin hankali kuma muna kokarin tuntubar sa kan yadda za mu kai masa cikon Naira miliyan 10 din. Al’ummarmu na cikin tsananin tashin hankali.”
Turji ya sa wa mutanen Moriki haraji
Aminiya ta gano cewa wa makonnin baya ne Turji ya kakaba wa mutanen Moriki, gari mafi girma a Karamar Hukumar Zurmi, harajin Naira miliyan 20 da matsayin ‘kudin kariya’
Dan ta’addan ya yi wa al’ummar garin da ’yan bindiga suka addaba da hare-hare da kisan gilla, alkawarin cewa idan suka biya kudin a cikin mako biyu, to zai daina kai musu hari, kuma manoma na iya zuwa gonakinsu su yi aiki ba tare da wata fargaba ba.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa tun bayan harin da jiragen soji suka kai sansanin Turji a kusa da kauyen Fakai da ke Karamar Hukumar Shinkafi a watan Satumba, ya addabi Moriki da kauyukan da ke makwabtaka da garin.
“Bayan ya sanya mana haraji muka zauna da mutanen garin kan yadda za mu tara kudin da ya nema, saboda mun san abin da zai iya biyowa baya idan muka ki yin abin da ya nema.
“Daga nan muka amince kowane gida a garin ya biya N6,500, wanda idan kowa ya biya za mu iya tara miliyan N20 da ya nema mu kai masa kafin cikar wa’adin.
“Amma hakan bai yiwu ba, sai miliyan N10.6 muka iya hadawa saboda wasu sun ki bayarwa.
“A cikin kudin kuma mun yi amfani da N100,ooo muka saya musu kwalayen sigari da burodi da lemun kwalba da katin waya, kamar yadda suka umarce mu.
“Muka hada mutum bakwai muka tura su domin su kai kudin a inda aka yi alkawarin haduwa da su a kusa da kauyen Kasayawa, mai nisan kilomita daya daga garin Moriki.
“Bayan sun isa wurin, wasu yaran Turji su 17 suka zo a kan babura suka bukaci a ba su kudin da sauran kayayyakin.
“Da aka sanar da Turji cewa kudin da aka kawo N10.5m ne ba N2om da aka yi alkawari ba sai ya fusata, ya umarci yaran ans ada su rike biyar daga cikin ’yan sakon su kai su Dajin Jirari,” in ji Sani.
Mun yi kokarin samun karin bayani daga kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, amma ya ce mana zai bincika ya ji mene ne ainihin abin da ya faru.