Kasurgumin dan bindigar nan da ya addabi wasu yankunan Jihar Zamfara, Bello Turji, ya nemi ya ajiye makamansa don a tsagaita zubar da jini daga dukkan bangarorin biyu.
A watan da ya gabata ne Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin murkushe ’yan ta’adda gaba daya, bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ayyana ’yan bindigar a matsayin ’yan ta’adda.
- ‘China ba za ta kwace kadarorin Najeriya ba saboda taurin bashi’
- An ceto mutum 5 daga hannun masu garkuwa da mutane
A cikin wasikar dai mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Disamban 2021, Turji ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar, Bello Matawalle da kuma Sarkin Shinkafi, kan bukatar tasa.
Ga hotunan wasikar:
Wani mazaunin garin Shinkafi, wanda mamba ne a kwamitin zaman lafiya na garin, ya tabbatar wa Aminiya sahihancin wasikar mai shafi uku ranar Lahadi.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da dan bindigar ke aike wa yankunan wasika ba.
Ko a watan Satumban da ya gabata, ya rubuta wata wasika da shi da wani dan bindigar, Halilu Sububu, suna gargadin mutane cewa za su zafafa kai musu hare-hare.
Neman sulhun nasa dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaron Najeriya suka zafafa kai hare-hare ga ’yan bindigar ta sama da kuma ta kasa.
Aminiya ta rawaito cewa a tsawon makon da ya gabata, an kai akalla hare-hare guda biyar a wuraren da Turji yake da sansani, inda yaransa da ’yan uwansa da dama suka halaka.