✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tunawa da marigayi Janar Shehu Musa ’Yar aduwa

Hausawa na cewa, ba rabo da gwani ba, mai da gwani irinsa. Marigayi Manjo Janar Shehu Musa ’Yar’aduwa (Allah Ya jikansa; Ya yafe masa, ya…

Hausawa na cewa, ba rabo da gwani ba, mai da gwani irinsa. Marigayi Manjo Janar Shehu Musa ’Yar’aduwa (Allah Ya jikansa; Ya yafe masa, ya rasu ne a ranar 8 ga watan Disamba,1997).  Yana daya daga cikin manyan kasar nan da tarihi ba zai taba mantawa da su ba, musamman yanzu da wasu halaye na dattako da sadaukarwa suka yi karanci a tsakanin matasan ’yan siyasa.

Shin me za mu koya daga rayuwa da gwagwarmayar wannan jarumi? Jarumtarsa, a matsayinsa na soja, wanda ya samu damar halartar makarantar horar da soja da ke Ingila wato Sandhurst, kuma da jarumtarsa da ya nuna a lokacin Yakin Basasar Najeriya. Koko za mu mai da hankali kacokan mu dubi tarihin siyasarsa, da irin gudunmawar da ya ba da a siyasance a Najeriya? Koko bangaren harkokin kasuwancinsa da nasarorin da ya samu a harkar kafa masana’antu za mu duba? Koko za mu dubi rawar da ya taka wajen yaki da kabilanci ko bangaranci? Ko juriya da jajircewa da ya nuna da ta kai shi rasa ransa a gidan wakafi? Ko ta ina mutum ya duba, zai ga lallai an yi jarumi, kuma nagartaccen mutum wanda ya daga sunan jiharsa, zuriyarsa da Najeriya baki daya.

Shakka babu, Shehu Musa ’Yar’aduwa, ya tashi daga gidan sarauta kuma gidan mulki, domin mahaifinsa, marigayi Musa ’Yar’aduwa, baya ga sarautar a Jamhuriya ta Farko shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya na wancan zamani wato Legas. To amma duk da kasancewar Shehu ya tashi cikin gata da wadata, za mu fahimci, yadda ya bambanta da takwarorinsa da suka tashi cikin gata da wadatar. Misali, akwai ’ya’ya da yawa da suka tashi cikin daula, suka samu dama, amma dama da daular ba ta amfane su ba. Hasali ma, sai suka rungumi miyagun dabi’u kamar shan giya da shaye-shaye da sace-sace da zinace-zinace a karshe ba su tsinana komai ba, kuma ba su dabbaka tarihin gidajen nasu ba. Rago, mashayi, dolo, lalatacce bai iya soja, ko ya yi, to ba zai yi tasiri ba, domin aikin soja, aiki ne na tarbiyya da jarumta. Wannan kawai ya isa, ya nuna maka, kowane ne Shehu Musa ’Yar’aduwa.

A soja ma, shi ba kurar baya ba ne domin ko a wancan lokaci da ke akwai dama da yawa, to ba kowa ne ake dauka a kai shi makarantar horar da sojoji ta Ingila Sandhurst ba. Duk matsayinka da gidan da ka fito.

Kashe Janar Murtala Ramat Mohammed, an samu sauyin gwamnati, inda Obasanjo ya zama Shugaban Kasa na mulkin soja, yayin da Shehu Musa ’Yar’aduwa ya zama Mataimakinsa.

Tarihi ya nuna gwamnatin  Obasanjo da Shehu Musa ’Yar’aduwa, ta nuna gaskiya wajen aiwatar da dukan tsare-tsaren da gwamnatin Murtala ta bari, muhimmi shi ne, mayar da Najeriya bisa turbar dimokuradiyya. Ba su bar gwamnati ba, sai da suka tabbatar an rubuta sabon kundin tsarin mulki, sannan suka shirya tsabtataccen zabe, suka mika gwamnati ga farar hula a ranar 1 ga watan Oktoba, 1979.

Kada mu manta gwamnatin Murtala da Obasanjo. gwamnati ce da ta ceto kasar nan daga mulkin Yakubu Gowon da bayan kammala Yakin Basasa ya kasa mayar da mulki ga farar hula. Mun san irin ci gaban da aka samu a lokacin Murtala da Obasanjo.

Fagen siyasa, za mu ga Shehu Musa ’Yar’aduwa tun Sardauna ba a kara kasurgumin dan siyasa a Arewa kamarsa ba. A Arewa ba a samu dan siyasa da ya samu karbuwa daga dukan sassan kasar nan -Yarbawa da Ibo da Kudu maso Kudu da Tsakiyar Najeriya. Ko’ina yana da yara, barori da abokan siyasa, masu bin bayansa. Ga irin  su Solomon Lar da Anthony Anenih, da Atiku Abubakar da Muhammadu Kwairanga Jada da Babagana Kingibe da sauransu. Wannan ya sa ake masa kirari a fagen siyasar Najeriya da ‘Gada mai hada zumunci’ (Bridge builder). Za mu ga tasirin siyasar Shehu Musa ’Yar’aduwa a lokacin tsarin mai da Najeriya mulkin dimokuradiyya na Janar Ibrahim Badamasi Babangida, inda Shehu ya kafa jam’iyyun PF da PDM, ya kuma assasa Jam’iyyar SDP, duk da haramta masa shiga siyasa da waccan gwamnati ta yi. Sannan ya taka rawa wajen ganin Cif MKO Abiola ya ci zabe a wancan lokaci.Wadansu na kamanta siyasar Shehu Musa ’Yar’aduwa da irin ta Awolowo, ni a fahimtata, siyasar Shehu Musa ’Yar’aduwa ta bambanta, tunda shi ne, ya fara yakar siyasar kabilanci ko shiyya a Najeriya.

Awolowo jam’iyyarsa ta AG, asalinta kungiyar kabilar Yarbawa ce wadda ake kira da Ogbe-Omo-Odudua. Kuma Awolowon nan, ya yi amfani da kabilanci a siyasar Jamhuriyya ta Farko, hatta a Jam’iyyar Matasan Najeriya (NYM) lokacin mulkin mallaka. Shi kuwa ’Yar’aduwa wadansu na ganin ya fi fifita wani yankin fiye da yankinsa.

Abin tambaya shi ne, yanzu yadda ake siyasar rashin alkibla, siyasar neman abinci da neman kudi, ko me ’Yar’aduwa zai ce da a ce zai dawo duniya?

Dubi  yadda ’yan siyasar yanzu suka raina mutane, yau suna waccan jam’iyya, gobe suna wata. Abin mamaki hatta tsofaffin ’yan siyasar da suka yi zamani da marigayi ’Yar’aduwa ba a bar su a baya wajen canja sheka babu gaira, babu dalili a wannan lokaci ba.

In da Shehu ’Yar’aduwa, irin wannan siyasar ya yi, to da lokacin da Babangida ya haramta musu shiga siyasa, sai ya zama munafuki, ma’ana, ya zama abin da ake kira “sycophant”, ya bi Babangida yana lallabarsa a tafi da shi amma maimakon haka, sai ya zabi ya mara wa Abiola baya, su yaki gwamnatin soja.

Da Shehu ’Yar’aduwa na siyasa mara kan gado irin wadda ake yi yanzu, da bai mutu a gidan yari ba. Da sai ya mika kai bori ya hau, ya bi Abacha, su sha dadi. Amma sai ya zabi ya tsaya bisa akidarsa. Shi ya sa yake cewa “Garkame ni da Janar Abacha ya yi, na daya daga cikin sadaukarwa da za mu yi, domin ’yantar da kasarmu”.

Marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa, kane ga Shehu ’Yar’aduwa, na daya daga cikin shugabannin Najeriya da tarihi ba zai taba mantawa da su ba..

Babu abin za mu ce yanzu sai Allah Ya jikan Shehu Musa ’Yar’aduwa, Ya sa kwanciya hutu ce.

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa  08165270879