✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tuna Baya: Tarihin shugaban ƙasar Najeriya: Janar Olusegun Obasanjo

Janar Olusegun Mathew Okikiola Ogunboye Aremu Obasanjo shi ne shugaban ƙasar Najeriya da yafi kowa daɗewa kan kujerar mulki. Ya zama shugaban ƙasa na mulkin…

Janar Olusegun Mathew Okikiola Ogunboye Aremu Obasanjo shi ne shugaban ƙasar Najeriya da yafi kowa daɗewa kan kujerar mulki.

Ya zama shugaban ƙasa na mulkin soji tsawon shekaru uku sannan daga baya ya dawo a matsayin shugaban mulkin farar hula tsawon shekaru takwas.

Ke nan ya yi shekaru Goma Sha Ɗaya akan kujerar mulkin Najeriya.

Tuna Baya: Tarihin Shugaban Mulkin Sojin Najeriya Janar Murtala Muhammad

Tuna Baya: Tarihin Shugaban Mulkin Sojin Najeriya Janar Yakubu Gowon

Obasanjo ya zama soja na farko a tarihin Najeriya da ya miƙa mulki ga farar hula.

Wannan abin ya sama masa ƙima a wurin ƙasashen duniya inda suka yi ta saka shi cikin ayyukan zaman lafiya na ƙasa da ƙasa.

Har ma ya nemi zama sakatare janar na Muajalisar Ɗinkin Duniya amma bai yi nasara ba.

Kuma bayan da sojoji suka hamɓarar da farar hula ya cigaba da sukar ƙudirinsu tare da rajin komawa mulkin dimokraɗiyya.

Ɗan fursuna

Kan haka ne shugaban ƙasa Janar Sani Abacha ya ɗaure shi a kurkuku bisa tuhumar yunƙurin yi masa juyin mulki.

Ya na kurkukun ne Abacha ya rasu shi kuma ya tsaya takarar shugaban ƙasa.

Bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa bisa tsarin dimokuraɗiyya ya mayar da hankali a wa’adin farko kan kyautata alaƙar Najeriya da ƙasashen ƙetare.

Tuna Baya: Tarihin shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Aguiyi Ironsi

Tuna Baya: Tarihin Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa

Ya samu barazanar siyasa ta cikin gida kafin ya koma kan wa’adin mulkinsa na biyu.

Daga nan ya mayar da hankalinsa kan siyasar Najeriya har ma ya yi yunƙurin gyaran tsarin mulki domin zarcewa a kan karagarsa.

Sai dai bai yi nasara ba, amma ya samu ya ɗora wanda yake so ta hanyar tafka maguɗin zaɓe.

Wannan ya sa darajarsa ta ragu a idon duniya amma ya cigaba da farfaɗo da ita ta hanyar sukan gwamnatocin da suka biyo bayansa.