Janar Abdulsalami Alhaji Abubakar shi ne shugaban mulkin soji na ƙarshe a Najeriya.
Ya mulki Najeriya tsawon shekara guda; daga 1998 zuwa 1999 bayan rasuwar Janar Sani Abacha.
- Tuna baya: Tarihin Janar Sani Abacha; Shugaban Najeriya #10
- Tuna Baya: Tarihin Chief Ernest Shonekan
Ya na daga cikin manyan hafsoshin sojin da basu taɓa riƙe muƙamin siyasa ba har zuwa lokacin da ya ɗare bisa kujerar mulki.
Ya kuma yi nasarar miƙa mulki ga farar hula, in da ya zama shugaban soji na biyu a tarihin Najeriya da ya yi hakan.