✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tuna baya kan rayuwar Alhaji Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa

A watan Agustan 1979 aka kaddamar da Hubbaren Tafawa Balewa a Bauchi.

Alhaji Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa shi ne ya kafa gwamnatin farko a ’yantacciyar Najeriya bayan Turawan Mulkin Mallaka sun ba kasar ’yanci ranar 1 ga Oktoban 1960.

Tun a zamanin Turawa ya zama Firayi Ministan Najeriya na farko a 1957.

Sannan jam’iyyarsa ta sake nasara a zaben 1959, lamarin da ya ba shi damar sake kafa gwamnati a 1960.

Ya kuma sake yin nasara a zaɓen 1964, amma bayan shekara biyu sojoji suka yi masa juyin mulki.

Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa ya yi suna bisa kawaici da karamci da yakana.

Haka kuma ana ji da shi wurin iya harshen Inglishi inda har ake yi masa laƙabi da ‘Golden Voice of Africa’.

Shi ne ya kafa harsasan duk wasu manyan ayyukan ci-gaba da ake ji da su a Najeriya ta yanzu kama daga tashar jiragen ruwa, manyan titunan mota da layin dogo da kuma tashar samar da wutar lantarki ta Kainji.

Sai dai mulkinsa ya sha fama da rikicin siyasa da ƙabilanci wanda shi ne ma ya jawo sojoji suka yi masa kisan gilla a lokacin da suka kifar da gwamnatinsa.

Ƙuruciya

An haifi Sa Abubakar ne a garin Tafawa Ɓalewa da ke Jihar Bauchi ta yanzu cikin watan Disamban 1912.

Mahaifinsa Yakubu ɗan Zala, ɗan ƙabilar Gerawa ne kuma shi ne Garkuwan Shamakin Ajiyan Bauchi Attahiru.

A 1922 Ajiya ya sa Abubakar a makarantar elemantare ta Tafawa Ɓalewa, amma bayan shekara uku sai aka rufe makarantar.

Don haka aka mayar da shi makarantar firamaren Lardin Bauchi da ke Yelwa.

A 1928 kuma ya yi nasarar tafiya Kwalejin Horar da Malamai da ke Katsina.

A wancan lokaci ita ce maƙurar karatun boko a Arewacin Najeriya.

Kuma wannan kwaleji ta Katsina ita ce ta zama maƙyanƙyasar shugabannin Arewacin Najeriya a zamanin Turawa da farkon samun ’yancin kai.

Abubakar Tafawa Balewa shi ne ɗalibi na 145 da aka ɗauka a makarantar.

Abokan karatunsa sun haɗa da Isah Kaita da Musa ’Yar’aduwa da Muhammad Habib Dikwa da Haruna Bashiru Gwandu da kuma Ahmadu Raɓah, wanda daga baya ya shahara da sunan Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.

A wannan kwalejin ne Abubakar Tafawa Ɓalewa ya fara koyon Ingilishi kuma kafin ya kammala sai da aka tabbatar cewa babu wanda ya kai shi a wannan fanni duk cikin ɗaliban kwalejin.

A nan ne kuma ya fara shugabanci, inda ya zama shugaban dalibai na ɗakin kwana mai suna Gabas House.

A 1933 ya kammala Kwalejin Katsina, inda ya samu satifiket na koyarwa mai daraja ta uku.

Malami marubuci

Bayan ya koma gida sai Gwamnatin Lardi a Bauchi ta ɗauki Abubakar Tafawa Ɓalewa ya zama malami a makarantar Midil ta Bauchi, inda ya koyar da Ingilishi da Tarihi da Tarihin ƙasa.

Ƙwarewarsa a Ingilishi ta sake bayyana ta yadda Turawan makarantar in sun zo da baƙi sukan so su bi da su ta bayan ajinsu sai baƙo ya ce ina kuka samu wani Bature a nan? Sannan ne za su nuna masa Malam Abubakar Tafawa Balewa.

Ranar 16 ga Satumban 1933 Abubakar Tafawa Balewa ya yi auren fari yana da shekara 21 a duniya.

Ya auri Hafsatu ’yar Malam Halilu Bafulatanin Bauchi wanda a lokacin yake Alƙali a Ningi. Ranar 28 ga Agustan 1934 ta rasu wurin haihuwa amma ’yar ta rayu, inda ya raɗa mata suna A’isha, amma ana kiran ta ‘Talle’.

Daga baya ya auri Huraira da Fatima (Matar Malam) da Tasalla da Kande da Kabo.

Amma duk ya sake su cikin shekara 10 saboda sun kasa kula masa da Talle.

Har ila yau, a 1933 ne Malam Abubakar ya zama marubuci.

Hukumar Adabi ta Arewacin Najeriya ce ta shirya gasar rubuta ƙagaggun labarai na Hausa.

Littafin Abubakar Tafawa Balewa mai suna Shaihu Umar shi ya zo na uku bayan Ruwan Bagaja na Abubakar Imam da Ganɗoki na Malam Bello Kagara.

Littafin ya nuna irin mummunan halin da bauta ke jefa al’umma ta hanyar ba da labarin wani yaro da aka sace shi aka sayar a matsayin bawa, inda wani Balarabe ya tafi da shi kasar Masar ya rike shi har ya zama Shaihun Malami.

Da yadda mahaifiyarsa ta shiga bulayin neman sa.

A 1943 Tafawa Ɓalewa ya zama Shugaban Makarantar Midil ta Bauchi bayan ɗalibai sun yi zanga-zanga game da cinye musu kuɗin kashewa da wancan shugaban ya yi.

A wannan shekarar ce kuma ya samu Babban Satifiket na Koyarwa a Fannin Tarihi.

A 1945 kuma Turawa suka tura shi Birtaniya tsawon shekara guda domin samun Babban Satifiket na Koyarwa a Cibiyar Horar da Malamai ta Jami’ar Landan.

Sun tafi ne tare da MalamYahaya Gusau da Malam Abdurrahman Mora da Malam Bello Dan’amar.

Fara siyasa

Tun kafin tafiyarsa Ingila, Abubakar Tafawa Ɓalewa ya fara sansana harkokin siyasa. Domin a 1943 ne Shugaban Lardi wato DO na Bauchi Mista A.J.Knott ya kafa Majalisar Taɗi ta Bauchi domin bai wa ’yan boko da sauran manyan gari damar tofa albarkacin bakinsu kan yadda ake gudanar da mulki.

Malam Abubakar shi ne yakan jagoranci zaman majalisar.

Malam Sa’adu Zungur da Malam Aminu Kano su ne kan gaba wurin sukar mulkin Turawa, amma a mafi yawan lokuta Malam Tafawa Ɓalewa kan goyi bayan Turawan.

Bayan gwamnati ta rusa majalisar saboda Malam Sa’adu ya ƙure Razdan sai aka kafa Jam’iyyar Ci-gaba ta Bauchi.

Amma Malam Abubakar bai shiga wannan jam’iyya ba.

A lokacin da yake Ingila ne Gwamnan Najeriya, Sa Arthur Richards ya bijiro da sabon kundin tsarin mulki wanda ya tanadi kafa majalisun dokoki na jihohi da kuma ta tarayya.

Bayan dawowarsa daga Ingila, Gwamnatin En’e ta Bauchi ta zaɓe shi cikin wakilan Majalisar Dokokin Jihar Arewa da ke Kaduna.

A ranar 20 ga Janairun 1947 aka kaddamar da majalisar a Kaduna.

A ranar kuma ’yan majalisar suka zaɓi waɗanda za su wakilce su a Majalisar Tarayya da ke Legas, inda a nan aka zaɓi Abubakar Tafawa Balewa da Bello Kano da Iro Katsina da Aliyu Makaman Bida da Yahaya Ilorin su zama wakilan Arewa a Majalisar Dokoki ta Tarayya da ke Legas.

A 1951 sabon tsarin mulki na Gwamna John Macpherson ya fara aiki, inda aka zaɓe shi ya zama wakili a Kaduna.

Daga nan kuma aka zaɓe shi cikin wakilan Legas, kuma ɗaya daga cikin ministoci uku daga Arewa tare da Muhamamdu Ribaɗu da Shettima Kashim.

Ranar 5 ga Janairun 1951 aka rantsar da shi ɗan Majalisar Tarayya, sannan ranar 17 ga watan kuma ya zama Ministan Ayyuka.

Hakazalika a shekarar aka ba shi lambar OBE.

A 1953 aka ƙara masa da sufuri bayan Minista Bode Thomas ya ajiye kujerarsa saboda rikicin neman ’yancinkai a 1956.

Wannan rikici shi ya jawo sake sabon taron tsarin mulki a Landan a 1953, kuma Malam Abubakar Tafawa Ɓalewa na daga cikin wakilan Arewa.

A watan Afrilun 1954 aka yi zaben shugabannin Jam’iyyar Mutanen Arewa ta NPC na farko, kuma na ƙarshe a Jos, inda aka sanar da Abubakar Tafawa Ɓalewa a matsayin Mataimakin Shugaba, yayin da Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya zama Shugaba.

Bayan zaben 1954 aka sake tabbatar masa da mukaminsa.

A 1957 suka koma Landan taron tsarin mulki, inda aka amince a bai wa Najeriya mulki a 1960. A wannan shekarar kuma ya sauke farali.

Firayi Minista

Ranar 2 ga Satumban 1957 ya zama Firayi Minstan Najeriya na farko, kasancewarsa Shugaban Jam’iyyar NPC a cikin majalisa. Ya kafa gwamnatin haɗa-ka, inda ya ɗauko ministoci 6 daga NCNC, 4 daga NPC, biyu daga AG da guda daga Cameroon National Congress.

A zaɓen 1959 NPC ce jagaba. Don haka ya zama Firayi Ministan ’yantacciyar Najeriya na farko ranar 1 ga Oktoba 1960.

A ranar kuma Sarauniyar Ingila ta ba shi lambar girma ta KCBE.

Firayi Minista Tafawa Ɓalewa ya yi rawar gani wurin sama wa Najeriya ƙima a ƙasasshen waje kuma shi ya jagoranci kafa Ƙungiyar Haɗa Kan Afirka (OAU).

Shi ne kuma ya jagoranci mayar da Tarayyar Najerjiya ta zama Jamhuriya a 1963.

Sai dai ya sha fama da rikicin cikingida, inda har ya sa dokar-ta-ɓaci a Jihar Yamma kuma a Nuwamban 1962 aka kama jagoran adawar Najeriya Cif Obafemi Awolowo da laifin yunƙurin juyin mulki.

A zaɓen tarayya na 1964 jam’yyyarsa ta samu rinjaye, amma Shugaban Kasa Dokta Nnamdi Azikiwe ya ƙi amincewa ya kafa sabuwar gwamnati sai da aka kai ruwa-rana.

A ranar 11 ga Oktoban 1965 aka yi zaɓen Majalisar Wakilai ta Jihar Yamma.

Zaɓen an yi rikici da ƙone-ƙone tare da ƙazamin maguɗi, inda aka sanar da Firimiya Akintola ya yi nasara.

Ranar 13 ga Oktoba aka rantsar da shi. Daga nan fa yaki har karshen gwamnati.

Daren Juma’ar ƙarshe cikin watan Ramadan wato 15 ga Janairun 1966 Manjo Emmanuel Ifeajuna ya jagoranci sojoji shida suka shiga gidan Tafawa Balewa suka yi awon gaba da shi.

Sai a ranar 20 ga Janairu aka gano gawarsa a hanyar Abeokuta kusa da Otta.

Ranar Asabar, washegari suka isa da gawar Bauchi ana gobe Sallah Ƙarama.

Ya rasu ya bar mahaifiyarsa da ’ya’ya 18 (da cikin Zainab ta 19) da gidaje biyu a Bauchi da Kaduna, sai kuma gona.

A 1973 gwamantin Janar Yakubu Gowon ta sa hotonsa a jikin takardar Naira.

Kuma a yanzu haka hotonsa ne a takardar Naira Biyar.

A watan Agustan 1979 aka kaddamar da Hubbarensa wanda Gwamnatin Tarayya ta gina a Bauchi.