An yi kira da kafofin watsa labarai da su karfafa rawar da suke takawa ta yaki da ta’addanci. Mataimakin Shugaban Kwamitin (PCNI) Alhaji Tijjani M. Tumsah ne ya yi wannan kira a lokacin da ya kai ziyara hedkwatar gidan rediyo da talabijin din da ke Jihar Kaduna.
Ziyarar na daga cikin zagayen da Kwamitin ke yi don wayar da kan al’umma a kan ayyukansa. Injiniya Abdulkadir Lere ne ya amshi tawagar kwamitin PCNI a madadin gidan rediyo da talabijin na Liberty. Ya ce kasancewar kafar watsa labarai ta Liberty tana da masu sauraro masu yawa ne ya sa kwamitin yake hulda da shi.
Lere wanda ya zagaya da tawagar don ganewa idanunsu irin na’urorin zamanin da Liberty take amfani da shi wajen watsa shirye-shiryenta ya jaddada aniyarsu na ci gaba da watsa shirye-shiryensu a harshen Hausa da Turanci a ciki da kuma wajen kasar nan.
A nasa jawabin Alhaji Tumsah ya hori gidan rediyon da Talabijin na Liberty da ya ci gaba da wayar da kan al’umma a game da yaki da ta’addanci musamman kasancewa wata kafa ce da ke da dimbin masu saurare a harshen Hausa a mafi yawa daga cikin Arewacin kasar nan.