✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tukuicin Girma ga mai azumi (3)

I’itikafi: I’itikafi shi ne mutum ya zauna a cikin masallaci domin yin sallolin nafila da karatun Alkur’ani da addu’o’i don neman dacewa daga Allah a…

I’itikafi:

I’itikafi shi ne mutum ya zauna a cikin masallaci domin yin sallolin nafila da karatun Alkur’ani da addu’o’i don neman dacewa daga Allah a duniya da Lahira. Shi kuma Sunnah ne da ake so, amma abin da aka fi so daga goman karshe na watan Ramadan. Kuma an ce karancinsa kwana daya da wuni daya, amma akasarinsa kwana uku. Awata ruwaya kuma an ce karancinsa kwana uku, amma mafi yawansa kwana goma har zuwa wata guda. Kowanne ka zaba daga cikin wadannan maganganu ya yi daidai. An karbo daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) ya kasance yana I’ittikafi a kwana goma na karshen Ramadan har ya bar duniya.”

Zakkar Fid-da-Kai:

ZakkarFid-da-Kai ita ce zakkar da ake yi idan aka kammala azumin Ramadan, an ce ya halatta a fitar da ita kafin a gama azumi da kwana uku ko kwana biyu, ko kwana daya ko a daren Sallah ko washegari ranar Sallah kafin a je masallaci. Domin an samu daga Dan Abbas (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya wajabta mana Zakkar Fid-da-Kai don tsarkakke mai azumi daga miyagun maganganu da kuma kura-kurai. Kuma ciyarwa ce ga talaka. Wanda ya ba da ita kafin a je masallacin Idi ya samu ladan zakka cikakke, amma wanda ya ba da ita bayan dawowa daga masallacin Idi, wannan yana da ladan sadaka ne kawai.”Abu Dauda ne ya ruwaito.

Ita Zakkatul Fidiri tana kan mai gida ne da wadanda suke karkashinsa kamar matarsa da ’ya’yansa maza da mata da ma’aikatan da suke karkashinsa.

Azumin da ake so mutum ya rika yi bayan na Ramadan:

1.  Guda shida a watan Shawwal, domin Annabi (SAW) yace:“Wanda yayi azumin watan Ramadan ya kuma yi shida a watan Shawwal, to, za a ba shi ladar wanda ya shekara yana azumi.”

2. Azumin Litinin da Alhamis: Saboda Annabi (SAW) yana yawaita azumi ranar Litinin da Alhamis, sai aka tambaye shi yaya kake yawaita azumi ranar Litinin da Alhamis sai ya ce a ranakun ne ake daukar ayyukan bayi zuwa gaAllah.

3.  Yin azumi uku kowane wata, ranar goma sha uku da sha hudu da sha biyar ga wata kuma suna da lada kamar mutum ya yi azumin shekara ne. Domin duk wani aikin alheri za a ba ka lada goma.

4.  Sai azumi guda tara da ake so mutum ya yi a watan Zul-Hajji da kuma guda daya na Ranar Arfa. Idan mutum ba aikin Hajji yake yi ba a wannan ranar.

5.  Azumin Tasu’a da Ashurawato azumin ranar tara da kuma goma ga watan dayana Musulunci(Muharram), shine ake cewa azumin Tasu’a da Ashura.

Azumin da aka hana yi:

1.  Azumi ranar kokwanto, (wato idan ba a tabbatar da ganin wata) a ranar 29 ga watan Sha’aban ba, dalili kuwa don ba a sani ba Ramadan ne ake ciki ko Sha’aban, saboda wannan shakkar ne aka hana yin azumi a wannan rana.

2. An hana yin azumi ranar Idi – Idil Fidiri (Karamar Sallah) ko Idil-Kabir (Babbar Sallah).An rawaito Annabi (SAW) yace: “Wanda ya yi azumi ranar Idi ya saba wa Baban Kasimu,(wato Annabi -SAW- ke nan don yana da da, da akekiransa da Alkasim, sai ake kiranAnnabi da Baban AI-Kasim

3. An hana azumi bayan Sallah da kwana daya kokwana biyu ko kwana uku.

4.  Kebe ranar Juma’a ita kadai da yin azumi shimaanhana.

5. Bai halatta ga mace ta yi azumin nafila ba sai daizininmijinta.

Nasihohi zuwa ga masu azumi:

Ya ’yan uwa Musuimi! Ku yi aiki da wadannan nasihohi:

1.  Ka yi azumin watan Ramadan kana mai imani da Allah kuma ka kyauta ta shi don a gafarta maka laifuffukanka da suka gabata.

2.  Kada ka yarda ka karya azumin watan Ramadan da gangan don yin haka yana daga cikin manyan laifuffuka.

3. Ka kuma tashi tsaye don yin SallarTarawihi, musamman a goman karshe wadanda ake samun Daren LailatuI Kadari a ciki don Allah (SWT) Ya ce: “Alherin da ke cikin LailatuI Kadari ya fi wata dubu.”

4.  Ka yi kokari abincinka da abin shanka su zamo na halal domin a karbi ayyukanka da addu’o’inka, kada ka yarda ka yi azumi sannan ka yi buda-baki da abin haram.

5.  Ka yi kokari ka ba wani abin buda-baki ko ya buda-baki da abincinka don ka samu daidai ladan azuminsa.

5.  Ka tsare salloli wato ka yi su a kan lokaci kuma tare da jama’a domin ka samu ladar jam’i kuma Allah Ya tsare ka daga musifar rayuwa.

7.  Ka yawaita sadaka domin sadakar da tafi lada, sadakar da aka yi a Watan Ramadan.

8.  Ka tsare muhimmancin lokacinka domin ayyuka nagari, don lokaci ya fi kudi tsada, don za a tambaye ka lokuta da aka ba ka me ka yi da shi kuma za ayi maka hisabi a kansa, daga karshe kuma a saka maka aikin da ka yi a rayuwarka, na alherikona sharri.

9. Ka je Umara in kana da hali a cikin watan Ramadan domin Umara a Ramadan tana daidai da aikin Hajji.

10. Ka yi kokari ka yi Sahur, idan so samu ne ka yi hakuri zuwa karshen dare kafin ketowar alfijir, domin Allah yana sanya albarka a cikin Sahur.

11. Ka gaggauta buda-baki da zarar rana ta fadi domin ka samu yardar Allah.

12. Ka yi kokarin yin wankan janaba in ka sadu da iyalinka a cikin daren azumi don ka samu damar yin Sallah cikin tsarki da tsabta cikkakiya tare da jama’a.

13. Ka yi amfani da damar da ka samu a cikin Ramadan, don ka dukufa ga karatun AIkur’ani domin ya zama hujjarka, ba hujja a kanka ba, kuma ya zama mai cetonka ranar tashin AIkiyama.

14.  Ka tsare harshenka, kada ka yi karya kuma kada ka la’anci wani kuma kada ka yi gibar wani. Kuma ka tsare idonka, ka tsare kunnenka daga jen kade-kade da wake-wake da raye-raye da wasanni kuma ka tsare hanunka daga sata ko daukar abin da banaka ba. Ka tsare kafarka zuwa in da bai dace ba a shari’a; domin azumi ba wai barin ci ko sha ba ne kawai, a’a kamewa ne daga dukkan abin da Allah Ya haramta, wannan shi ne hakikanin ma’anar azumi.

15. Ka yi kokari ka danne zuciyarka, ka yi hakuri, kajure, kuma ka daure kada ka yi fadace-fadace da zage-zage: ka yi kokari ka zama natsatse, amintacce don ka samu ladar azumicikakke.

16. Ka yi kwadayin samun tsoron Allah, a cikin azumin a sarari da boye ka rika tuna Shi ka kuma gode maSa saboda ni’imomin da Ya yi maka, kuma aikata dukkan abubuwan da Ya umarce ka, kuma ka nisanci duk abin da Ya hana.

17. Ka yawaita tuba zuwa ga Allah don neman gafararSa, ka kuma rokiAljanna, ka kuma nemi tsari daga wuta a koyaushe musamman a lokacin bude-baki da sahur, domin suna daga cikin lokuta masu muhimmanci.

Imam (SP) Ahmad Adam Kutubi na Rundunar ’Yan sandan Najeriya,

Za a iya tuntubarsa ta:

08036095723