Nafilfilin dararen goma na karshen watan Ramadan:
Daga A’isha (Allah Ya yarda da ita),ta ce: “Annabi (SAW), ya kasance idan goman karshe na watan Ramadan ya zo, to ba ya barci, sai ya tada mutanen gidansa maza da mata ya dukufa da nafilfili har karshen watan Ramadan.” Buhari ya ruwaito.
I’itikafi:
Shi I’itikafi shi ne mutum ya zauna a masallaci don nafilfili da karatun AIkur’ani da zikiri da addu’o’i don neman dacewa daga Allah a duniya da Lahira. Shi kuma Sunnah ne da ake so, amma abin da aka fi so daga goman karshe na watan Ramadan. Kuma an ce karancinsa kwana daya da wuni, amma akasarinsa kwana uku. Awata ruwaya kuma an ce karancinsa kwana uku, amma mafi yawansa kwana goma har zuwa wata guda. Kowanne ka zaba daga cikin wadannan maganganu ya yi daidai. An karbo daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Annabi (SAW) ya kasance yana I’ittikafi a kwana goma na karshen Ramadan har ya bar duniya.
Zakkar Fid-da-Kai:
ZakkarFid-da-Kai ita ce zakkar da ake yi idan aka gama azumin Ramadan, an ce ya halatta a fitar da ita kafin a gama azumi da wuni uku ko biyu, ko daya ko a daren Sallah ko ranar Sallah kafin a je masallaci. Domin an samu daga dan Abbas (RA) ya ce: “Annabi (SAW) ya wajabta mana Zakkar Fid-da-Kai don tsarkakke mai azumi daga miyagun maganganu da kuma kura-kurai. Kuma ciyarwa ce ga talaka. Wanda ya ba da ita kafin a je masallacin Idi ya samu ladar zakka cikakke, amma wanda ya ba da ita bayan dawowa daga masallacin Idi, wannan yana da ladar sadaka ce kawai.”Abu Dauda ne ya ruwaito.
Ita Zakkatul Fidiri tana kan mai gida ne da wadanda suke karkashinsa kamar matarsa da ’ya’yansa maza da mata da ma’aikatan da suke karkashinsa.
Azumin da ake so mutum ya rika yi bayan na Ramadan:
1.Guda shida a watan Shawwal, domin Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya yi azumin watan Ramadan ya kuma yi shida a watan Shawwal, to, za a ba shi ladar wanda ya shekara yana azumi.”
2. Azumin Litinin da Alhamis: Saboda Annabi (SAW) yana yawaita azumi ranar Litinin da Alhamis, sai aka tambaye shi yaya kake yawaita azumi ranar Litinin da Alhamis sai ya ce a ranakun ne ake daukar ayyukan bayi zuwa gaAllah.
3.Yin azumi uku kowane wata, ranar 13 da 14 da 15 ga kowane wata, kuma suna da lada kamar mutum ya yi azumin shekara ce. Domin duk wani aikin alheri za a ba ka lada goma.
4. Sai azumi guda tara da ake so mutum ya yi a watan Zul-Hajji da na Ranar Arfa. Idan mutum ba aikin Hajji yake yi ba.
5. Azumin Tasu’a da Ashura wato azumin ranar tara da goma ga watan Muharram, shi ne ake cewa azumin Tasu’a da Ashura.
Imam DSP Ahmad Adam Kutubi, 08036095723
Tukuici ga mai azumi (4)
Nafilfilin dararen goma na karshen watan Ramadan:Daga A’isha (Allah Ya yarda da ita),ta ce: “Annabi (SAW), ya kasance idan goman karshe na watan Ramadan ya…