✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tubar Bello Turji ba zai gaskata ba sai ya ajiye makamai —Gwamnatin Zamfara

Bayan shekara biyu kenan da bullo da shirin, wasu daga cikin ‘yan fashin sun koma daji sun sake daukar makamai.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa, ba za ta tabbatar da gaskiyar tuban kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ba, har sai ya fito ya ajiye makamansa a bainar jama’a.

Da yake jawabi a ranar Talata a Gusau, shugaban kwamitin kwance damarar ’yan bindiga a jihar Abdullahi Shinkafi, ya ce ba zai shiga wata tattaunawa da ‘yan bindiga ba, domin yawancinsu ba su da gaskiya.

Wannan dai na zuwa ne bayan shekara biyu kenan da bullo da shirin sulhu da ’yan bindiga, inda an samu wasu daga cikinsu sun koma daji sun sake daukar makamai.

A ranar Asabar da ta gabata ce, Mataimakin Gwamnan jihar, Hassan Nasiha ya sanar cewa, Turji ya rungumi shirin tattaunawar zaman lafiya, sannan ya yi alwashin fara kaddamar da farmaki kan sauran ‘yan bindiga a yankin Shinkafi da ke jihar.

Mataimakin gwamnan ya ce tun bayan da suka cimma matsaya game da tuban dan bindigar, yanzu fiye da makonni shida ke nan ba a sami asarar rai ba da ya danganci ayyukan ’yan ta’adda a jihar.

A yanzu haka dai Turji ya sanar da bukatar a sako masa ’yan bindigar da ke hannun gwamnati da kuma kawo karshen kisan da ya ce ana yi wa fulani ’yan uwansa.

A watan Yunin da ya gabata ne Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya umurci mataimakinsa da ya jagoranci tattaunawar sulhu da ’yan bindigar.

Wannan na zuwa ne matsayin yunkurin gwamna Matawalle na ribatar shirin rungumar sulhu da ‘yan bindigar.

A shekarar 2020 ce Gwamnatin Zamfara ta bullo da shirin sulhun a matsayin hanya daya tilo ta kawo karshen hare-haren ’yan bindigar da suka dauki tsawon shekaru 10 suna kaddamar wa al’umma tare da sace shanu baya ga garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

An dai samu wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan bindiga da suka mika kansu ga hukuma kamar irinsu Auwalun Daudawa wanda ya kitsa sace daliban makarantar Kankara da ke jihar Katsina a cikin watan Disamban 2020, inda har ya ajiye makamansa a bainar jama’a.