✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsuguno bata kare ba: Salah ya samu damar daukar fansa a kan Mane

Wannan wasanni za su bai wa Salah damar daukar fansa a kan Sadio Mane.

Jadawalin wasannin neman tikitin shiga gasar Cin Kofin Duniya da za ta gudana a kasar Qatar a badi, ya nuna cewar Masar da Senegal za su sake kece raini a cikin watan Maris, inda kowace kasa za ta yi tattaki zuwa gidan abokiyar hamayyarta.

Wannan ya nuna cewa bayan karawar da suka yi a wasan karshe na gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta AFCON 2021 da aka kammala a kasar Kamaru, tsuguno ba ta kare wa taurarin kwallon kafar kasashen Masar da Senegal ba, wato Sadio Mane da kuma Mohammed Salah, la’akari da cewar nan gaba kadan za su sake fafatawa a wani fagen na daban.

Masu sharhi a kan wasannin kwallon kafa na ganin wannan wasanni za su bai wa Salah damar daukar fansa a kan Sadio Mane domin huce takaici, inda dan wasan a jawabin da rarrashi da ya yi wa ’yan tawagar kasarsa bayan rashin nasara a wasan karshe na AFCON 2021, da su jajirce don ganin sun rama wa kura aniyyarta.

“Mun buga wasanni hudu duk na tsawon minti 120 cikin kimanin kwanaki 12 kacal, amma duk wannan yanzu ya zama tarihi.

“Muna da wasanni da wasu a watan gobe, kuma da Yardar Allah za mu dauki fansa a kansu,” inji Salah.

A sauran wasannin neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya a Qatar, Ghana za ta kara da Najeriya, Kamaru da Algeria, Mali da Tunisia, sai kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da za ta fafata da Morocco.

Sai dai fafatawar da za a yi  tsakanin Masar da Senegal ake sa ran za ta fi daukar hankali, la’akari da fitattun ‘yan wasan gasar Firimiyar Ingila Salah da kuma Mane wadanda suka barje gumi a wasan karshe na gasar AFCON.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Lahadin da ta gabata aka kammala Gasar Cin Kofin Afirka ta 2021, inda kasar Senegal ta doke kasar Masar a wasan karshe a bugun fenareti da ci hudu da biyu.

Wannan shi ne karo na farko da kasar Senegal ta lashe gasar a tarihinta, duk da cewa shekaru biyu da rabi da suka wuce ta kai wasan karshe, inda Aljeriya ta doke ta.

Sadio Mane ne ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasa na gasar, inda takwararsa Edourd Mendy ya lashe Gwarzon Gola, sannan Vincent Abubakar na tawagar Kamaru ya lashe kyautar dan wasa mafi zura kwallaye da kwallo 8 a gasar.