✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsoron da ya fi karfin tsaro

A yayin da gwamnati ke ta kokari domin ta tabbatar da samar da tsaro da nufin kawar da tsoro a tsakanin jama’a yadda za su gudanar…

A yayin da gwamnati ke ta kokari domin ta tabbatar da samar da tsaro da nufin kawar da tsoro a tsakanin jama’a yadda za su gudanar da harkokinsu cikin walwala da annashuwa, al’amarin sai kara tabarbarewa yake yi wanda ya sanya a halin yanzu amince wa juna ya yi karanci.

A halin yanzu babu yarda a tsakanin mutane, dan uwa yana jin tsoron dan uwansa, mahaifi yana jin rsoron dansa, da yana jin tsoron mahaifansa, aboki yana jin tsoron abokinsa, da sauransu.

Saboda tsoron juna da ake yi, wata rana wadansu mutane su biyu a mota sun tashi daga garin Kachiya a Jihar Kaduna za su tafi Kaduna, a kan hanyarsu sai wani Bafulatani ya tsayar da su, suka tsaya domin su dauke shi a matsayin fasinja, da Bafulatanin ya leka motar ya gan su, sai ya ce su tafi ya fasa tafiyar. Bayan sun yi gaba kadan sai wani mutum dan kabilar Ibo ya tsayar da su suka tsaya suka dauke shi, amma tunda ya shiga motar sai gabansu ya yi ta faduwa, suka yi tsit, babu wanda ya iya yin magana har suka isa Sabuwar Tasha a garin Kaduna, wannan fasinjan da suka dauko ya ce zai sauka.

Bayan sun sauke shi kafin su tashi sai ga wata mota ta tsaya, sai suka ga Bafulatanin nan da ya ki shiga motarsu ya fito daga cikin motar. Sai suka matsa kusa da shi suka ce ‘Ba kai ne muka tsaya za mu dauke ka a Kachiya ka ce, ka fasa tafiyar ba?’  Sai ya ce musu ‘Ai kun ba ni tsoro ne.’ Sai su ma suka ce masa ‘ ai mu ma mun dauko wani wanda ya ba mu tsoron.’ Suka fashe da dariya suka wuce.

To a haka yanzu ake zaune, da zarar an ga wani Bafulatani a daji sai a rika dari-dari da shi, shi ma yana dari-dari da wadanda ya gani.

A shekarun baya a yankin Arewacin kasar nan sata ce ta yi kamari, fashi da makami bai yawaita ba, sai dai a rika jin labarinsa a yankin Kudancin kasar nan. Daga baya sai fashi da makami ya kunno kai, a hankali har ya zama ruwan dare a yankin Arewa, mutane suna cikin tafiya sai a ce ’yan fashi sun tare hanya, matafiya sai su yi cirko-cirko a hanya har sai ’yan fashin sun gama abin da suke yi sun tashi ko kuma jami’an tsaro sun tarwatsa su. Da tafiya ta yi tafiya kuma saboda shigowar ci gaban zamani yanzu mutane ba su cika tafiya da makudan kudi ba saboda akwai katin ATM da kuma tsarin aikewa da kudi ta banki mai sauki kuma mutum zai iya karbar kudinsa a kowane reshe na bankin da yake da asusu, da sauran abubuwa da aka fito da su wadanda suka rage amfani da kudi kai-tsaye. Hakan ya sanya mutane ba su cika ajiye kudi a gida ba kuma ba su yawo da su, saboda haka sai aka fito da sabon salo na yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, wato dole a fito da kudi duk inda suke a ba masu garkuwar ko kuma su kashe wanda suka yi garkuwa da shi. Wani lokacin ma ko an ba su kudin sai sun kashe wanda suka kama.

Wannan masifa ta garkuwa da mutane ita ce take addabar jama’a a halin yanzu, wanda ya sanya harkokin kasuwanci  suka raunana da harkar noma, domin za a bi mutum har gona a sace shi ko kuma a ce masa kada ya sake zuwa gonar.

Duk wadannan bala’o’in suna faruwa ne saboda rashin gaskiya da cin amana da rashin cika alkawari da suka samu gindin zama a tsakanin jama’a, domin yanzu wanda yake da kudi shi ne mutumin kirki, shi ne ake girmamawa, sarakuna shi suke nada wa sarauta, malamai shi suke yi wa addu’a ta musamman, babu ruwan jama’a da tunanin inda ya samo kudin, shi ya sanya kowa ya himmatu wajen neman kudi ta kowane hali, ko halal ko haram ne babu damuwa.

Sabanin shekarun baya da al’umma ke kyamar mutumin da aka gani da dukiya amma ba a san asalinta ba. Hatta iyaye idan dansu ya kawo musu kudi ko wani abu mai daraja sai sun tambaye shi ya yi musu bayanin yadda ya samo su, idan bai yi bayani mai gamsarwa ba sai su kore shi da abin, amma yanzu iyaye ba su bincike sai dai su sanya wa dan nasu albarka, sai idan liki ya tashi sannan ido ya raina fata.

Ya kamata lallai mutane su koma ga Allah, su himmatu wajen yin addu’a domin Allah Ya yaye mana wannan halin da muke ciki na tsoron juna da zaman dar-dar.

Yanzu ga masifu iri-iri sun addabi jama’a kamar su Boko Haram da garkuwa da mutane da sara-suka da fashi da makami  da satar  shanu da sauransu.

Wani abin takaici shi ne idan mutum ba ya da dukiyar ma ba zai zauna lafiya ba, domin idan masu garkuwa suka kama mutum ba su raga masa saboda shi talaka ne, hasali ma dai idan suka fahimci ba ya da kudi to ya shiga uku, domin zai ci dan karen duka ko kuma su kashe shi.

Ya Allah! Ka yi mana maganin wadannan musifun, Ya Allah! Ka shiryar da masu musguna wa bayinKa, Ka tausasa zukatansu. Domin al’amarin yana neman ya gagari jami’an tsaro saboda su ma a tsakaninsu akwai rashin yarda da juna, don an sha kama jami’an tsaro suna hada kai da ’yan ta’adda, wanda hakan ya cusa tsoro a zukatan jama’a saboda masu samar da tsaron su ma sun zama abin tsoro. Wato tsoro yana neman ya fi karfin tsaro ke nan.