✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsokaci dangane da zumunci da muhimmancinsa

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan kammalalliyar godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya ce, “Ya ku mutane, ku bi Ubangijinku da takawa,…

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan kammalalliyar godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya ce, “Ya ku mutane, ku bi Ubangijinku da takawa, Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma’auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata.  Kuma ku bi Allah da takawa, Wanda kuke rokon juna da (sunan) Shi, da kuma ZUMUNTA.  Lallai ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.” (Suratun Nisa’i, aya ta 1).
Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawanSa kuma ManzonSa, Annabi Muhammadu dan Abdullahi Balarabe Bakuraishe, wanda ya ce, “Duk mai son arzikinsa ya karu, rayuwarsa ta tsawaita, to YA KYAUTATA ZUMUNTARSA.” (Buhari da Muslim suka ruwaito). Tsira da aminci ya kara tabbata gare shi da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa har zuwa Ranar karshe.
 Bayan haka, da yake an kammala shagulgulan Sallar Layya, kuma har yanzu akwai guggubin harkokin gaishe-gaishen Sallah a tsakanin ’yan uwa da abokan arziki, na ga zai kyautu a dan yi tsokaci dagane da muhimmancin karfafa sha’anin zumunci.
Kamar yadda aka gani a shadarar farko, an kawo ayar Alkur’ani Mai girma, wadda a cikinta aka yi zancen zumunta, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, a karkashin ayar, ya yi wani sharhi kamar haka: ‘Bin Allah Wanda Ya halitta ku, kira ga tabbatar da tauhidin Uluhiyya da Rububiyya (ne). Fitar mutane daga asali guda, wanda babu wani surki a cikinsa, yana tabbatar da girman jinsin mutum, kowane iri ne, kowane launi, kuma kowace halitta yake dauke da ita.  Tsoron Allah da tsaronSa a kan mutane yana wajabtar da tsayawa a cikin haddodin shari’arSa. Tsaron zumunta ko rantsuwa da ita, yana wajabtar da tausayi da rahama a kan halittar Allah, na kusa da na nesa. Hadisi ya nuna ba a yin rantsuwa da wanin Allah, saboda haka ma’anar ayar ita ce, “Ku ji tsoron Allah, ku tsare mahaifa da ZUMUNTA.”
Saboda haka, daga wannan ana iya gane cewa a nan an yi maganar mai tsoron Allah ne ke tsare ko kula da sadar da zumuntarsa.  
A cikin Hadisin da aka gabatar kuwa, za a iya fahimtar fa’idoji guda biyu a karkashin lamarin sadar da zumunta, wadanda suka kunshi karuwar arziki da kuma samun tsawon rai.  Dangane da tsawaitar rai dai, Allah Shi ne Mafi sani, Alkur’ani ya nuna mana cewa duk wanda aka kaddara masa iyakar rayuwarsa, to, ba a kara masa komai a kai, ba a kuma ragewa.  To, sai malamai suka ce, mafi kusancin ma’anar tsawaitar rai, ita ce mutum a ga yana yawaita ayyukan alheri a nan duniya, ko da kuwa bai dade a duniyar ba, domin ayyukan alheri ana nunnunka su ne daga 10 (goma) har zuwa 700 (dari bakwai), har iyakar abin da Allah Ya so Ya kara ko Ya nunka da kanSa.  
A nan mai karatu na iya fahimtar ko a kan wannan garabasar aka tsaya ma, ana iya cewa yana isa wajen a mayar da hankali kan tsare zumunta da kyautata zumunci.
A fannin ba kowa hakkinsa a cikin al’umma, Alkur’ani ya jero wadansu abubuwa masu muhimmanci, daya bayan daya, wadanda a cikinsu ya tabbatar da muhimmancin zumunta kamar haka: “Kuma ku bauta wa Allah, kuma kada ku hada wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatawa, kuma ga ma’abucin zumunta da marayu da matalauta da makwabci ma’abucin kusanta da makwabci manisanci da aboki a gefe da dan hanya da abin da hannuwanku na dama suka mallaka. Lallai ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai takama, mai yawan alfahari.” (Suratun Nisa’i aya ta 36).
Idan aka lura, kyautata zumunta (wato kyautata wa dangi) dangane da harkokin zamantakewa yana da mataki na uku daga tsoron Allah; kuma yana biye da matakin kyautata wa iyaye, kamar yadda Alkur’ani ya jero su; daga nan kuma sai sauran jama’a, wadanda ake mu’amala da su a harkokin yau da kullum.  Wannan kuwa ya dace da halin dan Adam da yakan karkata ga yi wa na kusa, kafin na nesa. Kuma ya dace da yanayin zamantakewar yau da kullum ta al’umma dangane da dauka da sauke nauyin wadanda ke tare da shi a rayuwa. Farko iyalinsa, sai dangi, sai kuma sauran jama’a, gwargwadon yadda hali ya bayar, a karkashin inuwar rangwame da tausayawa da jinkai da kauna da abokantaka, wadanda suke sinadarai ne na tabbatar da natsuwa da kyakkyawar rayuwa ga jama’ar duniya.
Kyautata zumunta na daga cikin manya-manyan kyawawan dabi’un Musulunci, kuma yana daga cikin abubuwan farko da Musulunci ya mayar da hankali wajen dabbaka su, tun daga lokacin da Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fara kira zuwa gare shi.
Zumunci yana daga cikin manyan sinadaran tsayar da shari’ar Musulunci.  Wannan kuwa yana kunshe ne a cikin wani dogon Hadisin Abu Sufyan (kafin ya musulunta) a yayin da yake hira da Hirkala (Sarkin Sarakunan Rum), lokacin da ya tambaye shi, “Me Manzon naku ya umurce ku da yi?” Sai Abu Sufyan ya ce, “Ya fadi mana, ‘Ku bauta wa Allah, Shi kadai, kada ku hada kowa da Shi (cikin bautar).  Ku bar addinin iyaye da kakanni.’ Ya ce mu yi Sallah, mu ba da sadaka (zakka), mu tsare mutuncinmu, kuma mu kyautata zumunta…” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).
Ana kidaya lamarin sadar da zumunta a cikin jerin manyan halayen Musulunci, wadanda suka hada ainihin kashin bayan addinin, wato kadaita Allah wajen bauta; da tsayar da Sallah; da yin gaskiya da tsare mutunci, duk wadanda ake bayyana wa wadanda suka yi tambaya dagane da addinin, a farko-farkon bayyanarsa.
Dogon labarin Amru dan Anbasah, (Allah Ya yarda da shi), wanda Imam Muslim ya ruwaito, shi ma ya dace da irin wannan tsari.  Ya ce, “Na shiga wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) a Makka (wato farkon bayyanar Musulunci), na ce, ‘Kai wane ne?’ Ya ce, “Manzo.” Na ce, ‘Mene ne Manzo?’ Ya ce, “Allah Ya aiko ni.” Na ce, ‘Da me Ya aiko ka?’ Ya ce, “Ya aiko ni in tabbatar da matsayin sadar da zumunta; in karya gumaka; kuma in karantar da cewa Allah daya ne (a wajen bauta) ba Shi da abokin tarayya…”
A cikin wannan yanki na Hadisi, ana iya fahimtar cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana matsayi da muhimmancin zumunta karara; ya daukaka matsayin, musamman tunda ya jera shi da wasu daga cikin manyan shika-shikan Musulunci.  Wannan ya tabbatar da matsayinsa da muhimmancinsa a cikin wannan addini, wanda Allah Ya saukar don jinkai ga al’ummar duniya gaba daya.
Ina ganin a dakata a nan, sai mako mai zuwa, in Allah Ya kai mu, mu ci gaba.  Wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh!